logo

HAUSA

Afrika CDC ta sake jaddada aniyar inganta tsarin kiwon lafiyar mata

2022-02-17 10:50:35 CRI

Afrika CDC ta sake jaddada aniyar inganta tsarin kiwon lafiyar mata_fororder_220217-A02-Africa CDC renews commitment to advancing women

Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika CDC za ta kulla hadin gwiwa da gwamnatoci, da shugabannin masana’antu da manyan kamfanoni domin daga matsayin tsarin kula da lafiyar matan nahiyar, babban jami’in hukumar ya bayyana hakan.

Benjamin Djoudalbaye, shugaban sashen tsare-tsare, hulda da sadarwa na Afrika CDC, ya ce suna bukatar zuba jarin da ake bukata wajen magance matsalolin cutukan dake shafar mata da matan dake matakin shekarun renon ciki da haihuwa.

Djoudalbaye ya ce, matan Afrika suna fuskantar wahalhalun fama da cutuka da yawan mutuwa don haka akwai bukatar a dora su kan sabuwar ajandar kiwon lafiya ta nahiyar. Ya bayyana hakan ne a taron da kungiyar kiwon lafiyar Afrika dake Nairobi ta shirya ta kafar bidiyo.

Ya ce za a gudanar da babban taron kungiyar kiwon lafiyar Afrika karo na bakwai cikin tsari mai inganci a ranar 24 ga watan Fabrairu a Nairobi, babban birnin kasar Kenya, taron zai kasance a matsayin wani dandalin musayar kwarewa wanda za a yi kyakkyawan amfani da shi wajen rage yawan mutuwar mata masu juna biyu a nahiyar Afrika. (Ahmad)