logo

HAUSA

Babban masanin aikin jaridar Najeriya ya bukaci kasarsa ta yi koyi da Sin

2022-02-17 16:44:03 CRI

Babban masanin aikin jaridar Najeriya ya bukaci kasarsa ta yi koyi da Sin_fororder_xi

A ranar 15 ga watan Fabrairun 2022, jaridar Leadership ta Najeriya ta wallafa wani sharhi da sanannen mai sharhi na Najeriya Ray Morphy, ya rubuta, mai taken, “Kasar Sin darasi ne da ya kamata Najeriya ta yi koyi", inda ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi nasarar fita daga kangin talauci da koma bayan ci gaba a cikin wasu gwamman shekaru ‘yan kadan. A cikin kankanin lokaci Sin ta cimma gagaruman nasarori na ban mamaki. Nasarorin da kasar Sin ta samu ya nuna cewa, muddin shugabanni suna da burika masu tasiri, tabbas ne za a samu gagarumin canji. Nasarorin da kasar Sin ta cimma a shirinta na kawar da talauci ya kara ilmantar da bil adama game da yaki da talauci, ya zama tamkar wani salon abin koyi ga duniya a yaki da talauci, kuma ya karawa dukkan kasashen duniya kaimi, musamman kasashe masu tasowa, game da shirin yaki da talauci.(Mai fassarawa: Ahmad daga CRI Hausa)