logo

HAUSA

Sin ta yi kira ga kasa da kasa da su kiyaye cudanyar kasa da kasa

2022-02-17 14:51:42 CRI

A jiya Laraba, kwamitin sulhun MDD ya gudanar da taro kan batun hadin gwiwar MDD da kungiyar CSTO. A jawabin da ya gabatar, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Zhang Jun ya yi nuni da cewa, ya kamata gamayyar kasa da kasa su kiyaye cudanyar bangarori daban daban, tare da nuna adawa ga kulla kawance a tsakanin wasu.

Zhang Jun ya ce, a yanzu haka, ta’addanci da tsattsauran ra’ayi da ma ra’ayin jawo baraka suna kara haifar da barazana, kuma ana kuma kara fuskantar matsalar laifuka da ake aikatarwa tsakanin kasa da kasa da ta miyagun kwayoyi, ga kuma annobar Covid-19 da ke addabar duniya, lamarin da ya sa kasashen duniya na kara fuskantar kalubale ta fannin tsaro da ci gaba. Baya ga haka, wasu kasashe kalilan sun yi ta nuna ra’ayi na kashin kai da fin karfin tuwo, tare da lalata tsaron sauran kasashe da ma ci gabansu, lamarin da ya lalata odar kasa da kasa da ma kwanciyar hankalin duniya. A cikin irin wannan hali, ya zama dole kasa da kasa su karfafa hadin kansu a maimakon a yi fito-na-fito, sa’an nan su karfafa zaman daidaito da amincewa da juna a tsakaninsu. Ta hakan kuma, za a iya kai ga kiyaye albarka da kwanciyar hankali da adalci a duniya. (Lubabatu)