logo

HAUSA

HAWA TEBURIN SHAWARA NE KADAI DAMAR KAWO KARSHEN TAKADDAMAR RASHA DA UKRAINE

2022-02-16 18:28:42 CRI

A baya bayan nan, cikin batutuwa mafiya jan hankalin sassan kasa da kasa, akwai ruruwar takaddama tsakanin kasashen Rasha da Ukraine, inda ya zuwa yanzu Rasha ta jibge dubun dubatar dakarun sojin ta a kan iyakar ta da gabashin Ukraine, a wani mataki da wasu ke kallo a matsayin shirin aukawa Ukraine din da yaki, yayin da a hannu guda, kasashen yamma da kawance kungiyar tsaro ta NATO ke tattara karfi waje guda, da nufin baiwa Ukraine din kariya, idan har Rasha ta yi yunkurin mamaye ta.

HAWA TEBURIN SHAWARA NE KADAI DAMAR KAWO KARSHEN TAKADDAMAR RASHA DA UKRAINE_fororder_220216世界22007-hoto3

A zahiri dai, burin Rasha shi ne kare martabar ta a yankin na turai, da wanzar da tasirinta ta fuskar tsaro, da dakile yunkurin Ukraine na shiga kungiyar tsaro ta NATO. Yayin da a hannu guda, Ukraine din ke fatan shiga NATO zai ba ta karin kariya da ‘yancin cin gashin kai.

HAWA TEBURIN SHAWARA NE KADAI DAMAR KAWO KARSHEN TAKADDAMAR RASHA DA UKRAINE_fororder_220216世界22007-hoto4

Yayin da sassan kasa da kasa ke ta gabatar da shawarwari game da yadda za a kaucewa tsunduma yaki, sakamakon wannan hali da ake ciki, tuni shugabannin manyan kasashen duniya, irin su shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, da shugaban Faransa Emanuel Macron, suka zanta da shugaban Rasha Vladimir Putin, tare da jaddada masa bukatar kaucewa shiga yaki, da fatan warware rikicin ta hanyar diflomasiyya.

HAWA TEBURIN SHAWARA NE KADAI DAMAR KAWO KARSHEN TAKADDAMAR RASHA DA UKRAINE_fororder_220216世界22007-hoto1

Wani abu mai karfafa gwiwa game da yanayin da ake ciki shi ne, yadda shi kan sa shugaba Putin din ya bayyana cewa, a bangaren Rasha, ba sa son shiga yaki, shi ya sa ma suka gabatar da shawarwarin yadda za a yi sulhu, da kokarin cimma yarjejeniyar da za ta tabbatar da tsaro ga kowa.  

Babban abun fata a yanzu, shi ne dukkanin sassa masu ruwa da tsaki a wannan takaddama ta Rasha da Ukraine, za su rungumi komawa teburin shawara, da amicewa sulhu, da yin hakuri da wasu bukatu domin wanzar da zaman lafiya mai dorewa, a wannan muhimmin yanki na nahiyar Turai.  (Saminu Hassan, Ahmad Fagam, Sanusi Chen)