logo

HAUSA

Kasar Sin tana kara jawo hankalin masu zuba jari

2022-02-16 21:04:27 CRI

Kasar Sin tana kara jawo hankalin masu zuba jari_fororder_sin

Kwanakin baya, ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar da alkaluma dake nuna cewa, a watan Janairun bana, ban da bangarorin banki, da na hada-hadar kudi da inshora, adadin jarin waje da ake amfani da shi a kasar Sin, ya kai dalar Amurka biliyan 15.84, adadin da ya karu da kaso 17.6 bisa dari, inda aka kwatanta da makamancin lokaci na bara.

Hakika ba ma kawai alkaluman sun nuna cewa, kasar Sin ta samu sabon ci gaba a farkon shekarar da ake ci ba ne, har ma ya nuna cewa, jarin waje na cike da imani kan kasuwar kasar Sin, wato kasar Sin tana kara jawo hankalin masu zuba jari.

Nan gaba kuma, kasar Sin za ta ci gaba da habaka bude kofa ga ketare, domin more damammakin bunkasuwar tattalin arziki mai inganci tare da sauran kasashen duniya. (Jamila)