logo

HAUSA

Idan Ba Za A Taimakawa Afghanistan Ba, Bai Kamata A Yi Mata Fin Karfi Ba

2022-02-16 19:47:17 CRI

Idan Ba Za A Taimakawa Afghanistan Ba, Bai Kamata A Yi Mata Fin Karfi Ba_fororder_微信图片_20220216170354

Idan Ba Za A Taimakawa Afghanistan Ba, Bai Kamata A Yi Mata Fin Karfi Ba_fororder_微信图片_20220216170401

Daga CRI HAUSA

Idan aka kira Afghanistan, na yi imanin babu abun da zai zo zuciyar mutane fiye da yake-yaken da ta yi fama da su da dimbin wahalhalun da jama’arta ke fuskanta. Sai dai, abun mamaki, a wannan gaba da kasar ke cikin mawuyacin hali ne, gwamnatin Amurka ta sanar da cewa za ta saki wasu kudaden kasar da a baya ta kakabawa takunkumi, wadanda yawansu ya kai dala biliyan 7, inda za ta yi amfani da rabinsu wajen biyan diyya ga mutanen da harin ranar 11 ga watan Satumban 2001 ya rutsa da su.

Idan ba a manta, al’ummar Afghanistan sun shafe gomman shekaru suna fama da yaki, haka zalika, Amurka ta kwashe shekaru 20 da sunan tana yaki da ’yan ta’adda a kasar. Kuma janyewar da ta yi a baya-bayan nan cikin watan Augustan bara, ya sa kasashen waje kakaba takunkumi kan kudaden ajiyar kasar da yawansu ya kai dala biliyan 10, kuma dala biliyan 7 daga ciki, yana Amurka. Wannan yunkuri kadai ya durkusar da tattalin arzikin kasar Afghanistan tare da jefa al’ummarta cikin mawuyacin hali.

Kasashe da hukumomin duniya na ta kira da a kare tattalin arzikin kasar daga durkushewa. Ko yayin taron kungiyar hadin kan Shanghai SCO da aka yi a watan Satumban da ya gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarwarin taimakawa kasar. Shi ma Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya yi irin wannan kira a watan Oktoba. Haka zalika kungiyar IOC ta kasashen musulmi, cikin watan Disamba, ta kafa asusun tallafawa al’ummar Afghanistan.

Abun takaici ne yadda Amurka ke kiran kanta da babbar kasa kuma mai martaba tsarin demokradiyya, ke bullo da hallayar da suka sabawa furucinta, wadanda ke bayyana irin son kai da rashin imaninta da kuma danniya ko fin karfi. Arzikin kasar Afghanistan, mallakin al’ummar kasar ne, su ne ya kamata a ce sun kasafta arzikinsu yadda ya dace a matsayin kasar na mai cikakken ’yanci, ba wai wata kasa ta nuna musu fin karfi ba. Ayyukan ta’addanci ta kowacce fuska, ba abu ne da za a lamunta ba. Babu wanda zai goyi bayan munanan hare-haren da aka kai wa Amurka a ranar 11 ga watan Satumba, haka kuma ba za a manta da wadanda hare-haren suka rutsa da su ba. Amma, bai kamata daukacin al’ummar Afghanistan su dauki alhakin abun da wasu ’yan tsiraru suka yi ba. Idan har Amurka ba za ta taimakawa kasar fita daga mawuyacin halin da take ciki, wadda ta taimaka wajen ingiza ta ba, to bai kamata ta ce za ta dauki rabin dukiyarta ko kuma ta zama mai sarrafa dukiyar kasar ba. Sam wannan bai dace ba, domin fin karfi ne. (Faeza Mustapha)