logo

HAUSA

Sin: Yayata batun yaki da Amurka ta rika yi ya rura wutar rikicin Ukraine

2022-02-16 19:14:46 CRI

A baya bayan nan, kasar Amurka ta rika yayata batun yiwuwar barkewar yaki tsakanin Rasha da Ukraine, lamarin da ya haifar da yanayi na dar dar, da koma bayan tattalin arziki da zamantakewar al’umma a Ukraine.

Kakakin ma’aikatar wajen kasar Sin Wang Wenbin ne ya bayyana hakan, yayin taron manema labarai da ya gudana a Larabar nan. Wang ya yi tsokacin ne, biyowa bayan yadda wasu kafofin watsa labaran yammacin duniya suka rika hasashen cewa, Rasha na iya aukawa Ukraine a Larabar nan.

Wang ya ce, irin wadannan kalamai, na cikin abubuwan da suka haifar da jan kafa, game da komawa teburin shawara da tattaunawa, tsakanin sassan da rikincin ya shafa. (Saminu)