logo

HAUSA

MDD ta yi kira da a yi amfani da diflomasiyya wajen shawo kan rikicin Rasha da Ukraine

2022-02-15 11:17:00 CRI

MDD ta yi kira da a yi amfani da diflomasiyya wajen shawo kan rikicin Rasha da Ukraine_fororder_220215-faeza-Ukraine

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya yi kira da a yi amfani da diflomasiyya wajen yayyafawa rikicin Rasha da Ukraine ruwa sanyi.

Antonio Guterres, ya ce ya damu ainun da dumammar yanayi da karuwar cece-kuce game da yuwuwar aukuwar yaki.

Ya ce jefa bil adama cikin damuwa da lalata tsaron nahiyar Turai da ma duniya baki daya, abu ne mai matukar tsanani, don haka ba za su amince da irin wannan fito na fito mai hadari ba.

Da farko a jiyan, Sakatare Janar din ya tatatuna ta kafar bidiyo da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov. Ya kuma yi wata tattaunawar ta daban, da ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba.  (Fa’iza Mustapha)