logo

HAUSA

An ceto mutane 20 da aka yi garkuwa da su a arewacin Nijeriya

2022-02-15 14:01:26 CRI

Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta ce an kashe ’yan bindiga da dama tare da ceto mutane 20 da suka yi garkuwa da su, yayin wani samame da jami’anta suka kai a baya-bayan nan a jihar Niger.

Kakakin rundanar ’yan sandan jihar Wasiu Abiodun, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, samamen ya gudana ne bisa hadin gwiwa da sojoji da ’yan banga, bayan samun sahihan bayanan sirri game da ayyukan ’yan bindigar a kauyen Nasko dake yankin karamar hukumar Magama ta Jihar Niger.

Har ila yau, rundunar ’yan sanda jihar Zamfara, ta sanar da ceto wasu mutane 5 da aka yi garkuwa da su a jihar.

Kakakin rundunar Muhammad Shehu, ya sanar da cewa, an ceto dukkan mutanen ne a ranar Litinin yayin wani aikin bincike da ceto da jami’an ’yan sanda suka yi a daji.

Ya kara da cewa, tawagar jami’an lafiya na rundunar da ta gwamnatin jihar, na aiki tare domin tabbatar da an duba lafiyar mutanen yadda ya kamata. (Fa’iza Mustapha)