’Yar wasan kasar Sin Xu Mengtao ta lashe lambar zinare a wasan Freestyle Skiing
2022-02-15 13:53:46 CRI
Jiya 14 ga wata, ’yar wasan kasar Sin Xu Mengtao ta zama zakara bisa maki 108.61 a wasan tseren kankara da ake sarrafa jiki a iska na Freestyle Skiing a gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi dake gudana a Beijing yanzu haka. Wannan ita ce lambar zinare ta biyar da tawagar ’yan wasannin kasar Sin ta samu a cikin gasar wasannin Olympics ta wannan karo, wadda kuma ta kasance lambar zinare ta biyu da kungiyar ’yan wasan tseren kankara da ake sarrafa jiki a iska ta Sin ta samu a cikin wasan, bayan shekaru 16 da suka gabata.
A cikin wasan tseren kankara da ake sarrafa jiki a iska, tawagar Sin ce ta fi samun yawan lambobin yabo a cikin gasannin Olympics na lokacin sanyi na baya, don haka ana mai da matukar hankali a kanta. Amma tun bayan da Han Xiaopeng ya zama zakara a wasan a shekarar 2006, Xu Mengtao ta sake cimma burin bayan shekaru 16. Xu mai shekaru 31 da haihuwa, wadda ta shiga gasannin Olympics har sau hudu, ta ce,
“Dalilin da ya sa na dage wajen yin wasan tseren kankara da ake sarrafa jiki a iska shi ne, ina matukar sha’awarsa, kuma ina da imanin cimma burina a gasar wasannin Olympics. Tun ina da shekaru 5 a duniya, nake burin samun lambar zinare a gasar wasannin Olympics. Wadda ke mara min baya ko da yaushe ita ce kasar Sin mahaifata.” (Kande Gao)