logo

HAUSA

Hadin Kan Afirka Da Sin Na Tabbatar Da Tsaron Abinci A Nahiyar Afirka

2022-02-15 20:41:55 CMG

Sharhi daga Bello Wang

A kwanakin baya an kawo karshen taron kolin kungiyar AU na 35 a kasar Habasha, inda mahalarta taron suka sanya wa shekarar 2022 da muke ciki taken “shekarar tabbatar da samun isashen abinci masu gina jiki”, don jaddada muhimmancin tsaron abinci a nahiyar Afirka. Hakika a cikin shekarar da ta gabata, annobar COVID-19 ta haifar da mummunar illa ga tattalin arzikin kasashen Afirka, lamarin da ya sanya mutanen kasashen kimanin miliyan 30 zuwa miliyan 40 fuskantar yunwa. Wannan yanayi ya hada da bala’i daga indallahi, sun sa ake fuskantar karuwar matsalolin rashin tsaron abinci da ta kai fiye da kashi 60%. Ganin wannan mawuyacin halin da mutanen kasashen Afirka ke ciki, ya sa ni, a matsayin wani Basine, fara tunanin matakan da kasar Sin za ta iya dauka, don taimaka wajen daidaita lamarin.

Hadin Kan Afirka Da Sin Na Tabbatar Da Tsaron Abinci A Nahiyar Afirka_fororder_gona-1

Sa’an nan bayan da na yi nazarin kan wasu bayanan da aka gabatar, na gamsu da huldar kut da kut da ake samu tsakanin bangarorin Afirka da Sin, ta fuskar aikin gona, inda ake ta kokarin sabunta ayyukan hadin kai a tsakaninsu. A taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da ya gudana a Senegal bara, kasar Sin ta yi alkawarin tura karin kwararru masu fasahohin aikin gona 500 zuwa kasashen Afirka, da ba da tallafin wasu ayyukan rage talauci da raya aikin gona guda 10 a nahiyar Afirka.

Hadin Kan Afirka Da Sin Na Tabbatar Da Tsaron Abinci A Nahiyar Afirka_fororder_gona-2

Don tabbatar da tsaron abinci, ya kamata a samar da karin amfanin gona. A wannan bangare, hadin gwiwar bangarorin Afirka da Sin a fannin fasahar aikin gona na taka muhimmiyar rawa. Misali a kasar Tanzania, farfesan jami’ar aikin gona ta kasar Sin, mista Li Xiaoyun, ya yi kokarin yayata wata sabuwar fasahar noman masara, wadda ta ba manoman kasar damar samu karin masara ba tare da zuba kudi don sayen magani da taki ba. Kana a Sao Tome da Principe, Xu Dazhou, wani kwararre dan kasar Sin a fannin aikin gona, ya horar da ma’aikata masu fasahar aikin gona na kasar kan bambanta cututtukan da su kan kama amfanin gona, da koyar da manoma yadda ake zabar maganin kashe kwari mai dacewa, ta yadda aka tabbatar da ingancin amfanin gona, da samun karinsu. Sa’an nan a kasar Mozambique, manoman wurin sun yi amfani da na’urori masu sarrafa kansu kirar kasar Sin wajen dasa iri, da fesa magani, inda aka samu damar kara saurin aiki, da sanya yawan hatsin da ake samu ya ninka. Wadannan abubuwa na cikin labarun da na karanta a kwanakin nan.

Hadin Kan Afirka Da Sin Na Tabbatar Da Tsaron Abinci A Nahiyar Afirka_fororder_gona-3

Ban da samar da karin amfanin gona, ya kamata a yi kokarin kyautata ayyukan noma, idan ana son tabbatar da tsaron abinci. Don cimma wannan buri, ana bukatar sayar da amfanin gonan da wani farashi mai kyau, da samarwa manoma da karin kudin shiga, ta yadda za su so habaka ayyukansu na samar da amfanin gona. A wannan bangare, kasar Sin ita ma na taka rawar gani, ta hanyar shigo da dimbin amfanin gona daga kasashen Afirka. Yanzu haka, kasar Sin ta zama ta biyu a duniya, a fannin shigo da amfanin gona daga nahiyar Afirka, inda karin kayayyaki, irinsu ridi, da gahawa, da yaji, da lemu, na shiga cikin kasuwannin kasar, har ma adadin kayayyakin ya karu da kashi 9.4%, a watanni 11 na farko na shekarar 2021. An ce, yadda kasar Sin ke shigowa da amfanin gonan Afirka na taimakawa nahiyar wajen daidaita illar annoba, da samun farfadowar tattalin arziki cikin sauri.

Hadin Kan Afirka Da Sin Na Tabbatar Da Tsaron Abinci A Nahiyar Afirka_fororder_gona-4

Sa’an nan don cimma burin tabbatar da tsaron abinci, ana bukatar daidaita wasu matsalolin dake bayan aikin gona, misali: tashin hankali. Hukumar abinci ta duniya ta gabatar da jerin sunayen wuraren da ke fama da yunwa, ciki har da wasu kasashe 3 dake nahiyar Afirka, wato Najeriya, Habasha, da Sudan ta Kudu. Dalilin da ya sa haka shi ne domin ana ta samun tashin hankali a wadannan kasashen 3. Misali, a arewa maso gabashin Najeriya, yake-yaken da kungiyar Boko Haram ta kaddamar sun sa kimanin mutane miliyan 4.4 fuskantar matsalar tamowa. To, ta yaya za a iya daidaita wannan matsala? Za a iya ci gaba da dogaro kan hadin gwiwar da ake yi tsakanin Afirka da Sin. Babbar manufar kasar Sin a fannin hadin kai da kasashen Afirka kan ayyukan tsaro ita ce “Bari kasashen Afirka su gabatar da bukata, da dauki mataki bayan da kasashen Afirka sun amince da haka, da baiwa kasashen Afirka matsayi na jagora”. Kana kasar tana neman daidaita matsaloli daga tushensu, inda ta mai da raya tattalin arziki cikin manyan ayyuka na tabbatar da zaman lafiya da tsaro. Aikin tsaro yana da matukar muhimmanci ga wata kasa, don haka yayin da suke kula da aikin, kasashen Afirka na bukatar hadin gwiwa da abokan hulda da za su iya dogaro a kansu, kana kasar Sin daya ce daga cikin abokan.

Abun da ya fi muhimmanci shi ne Sinawa su ma sun taba fama da yunwa. Har yanzu mamata ba ta manta da lokacin da take jin yunwa har ma ta kasa yin barci ba, a lokacin da take karama. Ko da yake Sinawa sun daidaita matsalar yunwa daga tushenta, ta hanyar yin gyare-gyare da bude kofar kasar, da raya tattalin arizki, da fasahohin noma, gami da kokarin tabbatar da wadatar bai daya ta daukacin al’ummar kasar, amma duk da haka, mutanen Sin na ci gaba da nuna sahihanci da karamci, yayin da suke ba da taimako ga abokansu da suke fama da matsalar yunwa. (Bello Wang)

Bello