logo

HAUSA

Sin ta yi kira ga sassan kasa da kasa da su kauracewa kambama batun rikicin Ukraine

2022-02-14 19:42:59 CRI

Sin na fatan sassan kasa da kasa za su kauracewa kambama batun rikicin kasar Ukraine, tare da kaucewa kara rura wutar sabani game da batun.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ne ya bayyana hakan, a Litinin din nan, yayin taron manema labarai da ya gudana.

Wang ya kara jaddada matsayin kasar Sin, don gane da takaddamar dake faruwa game da Ukraine, yana mai cewa, burin da ake da shi, shi ne dukkanin sassan da batun ya shafa, za su amince da matakan warware wannan lamari, ta hanyar gudanar da cikakkun shawarwari da tattaunawa.    (Saminu)