logo

HAUSA

Xi da takwaransa na kasar Mexico sun aika wa juna sakon murnar cika shekaru 50 da kafuwar huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu

2022-02-14 10:56:58 CRI

Xi da takwaransa na kasar Mexico sun aika wa juna sakon murnar cika shekaru 50 da kafuwar huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu_fororder_hotoSM

Yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Maxico Andres Manuel Lopez Obrador sun aika wa juna sakon murnar cika shekaru 50 da kafuwar huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu.

Xi Jinping ya ce, bayan kafuwar dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu, musamman ma, bayan kulla dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a shekarar 2013, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta bunkasa cikin sauri. Kuma, ana ci gaba da zurfafa fahimtar juna kan harkokin siyasa, da mu’amalar dake tsakanin kasashen biyu bisa fannoni da dama. Bayan barkewar annobar COVID-19, kasar Sin da kasar Mexico sun hada kansu da kuma taimakawa juna, inda suka nuna wa kasashen duniya abin koyi game da yin hadin gwiwar yaki da annoba.

Xi ya kuma jaddada cewa, yana son yin hadin gwiwa da shugaba Lopez, domin karfafa zamunci da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, ta yadda za su neman ci gaba tare. Haka kuma, yana fatan inganta dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu, ta yadda za a zurfafa zumuncin dake tsakanin jama’ar kasashen biyu.

A nasa bangare kuma, Lopez Obrador ya ce, a halin yanzu, ana ci gaba da karfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasarsa da kasar Sin, lamarin da ya tallafa wa al’ummomin kasashen biyu. Kuma, bangarorin biyu suna hada kansu wajen fuskantar kalubaloli daban-daban. Ya yi imanin cewa, tabbas ne, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu za ta ci gaba da samun bunkasuwa kamar yadda ake fatan. (Maryam)