logo

HAUSA

Karin mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a wannan mako a Nijar ya kai 25

2022-02-14 20:27:56 CRI

Jiya hukumar kiwon lafiya ta janhuriyar Nijar ta ba da rahoton cewa, karin mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a wannan mako a kasar ya kai mutane 25, yayin da kuma karin mutanen da suka warke daga cutar ya kai 204, kana karin mutum 1 ya rasu sakamakon harbuwa da cutar.

Tun barkewar cutar a kasar, yawan al’ummar Nijar da a yi musu gwajin cutar ya kai 222,936, yayin da aka tabbatar da cewa, mutane 8,711 sun kamu da cutar, daga cikinsu 8,362 sun warke, kana 303 sun rasa rayukansu. (Amina Xu)