logo

HAUSA

Taron manyan jami’ai 4 da Amurka ta kira ya kara fallasa manufar Amurka ta tada hargitsi

2022-02-14 20:15:10 CRI

Taron manyan jami’ai 4 da Amurka ta kira ya kara fallasa manufar Amurka ta tada hargitsi_fororder_美国-4

A baya bayan nan, kasar Amurka ta fitar da rahoton taron ganawar manyan jami’an kasashe 4 mai lakabin "U.S. Indo-Pacific Strategy", rahoton da ya kara tabbatar da manufar Amurka, cikin shekarun baya bayan nan, ta kambama zargin nan na kasancewar “Sin barazana”, da gayyatar kawayen ta domin hada wani gungu, da fatan yin hadin gwiwar dakile kasar Sin, ta yadda Amurka za ta cika burin ta na wanzar da danniya, da farfado da tasirin ta a yankin tekun Asiya da Fasifik, da ma sauran sassan duniya.

Don haka dai ta bayyana a fili, cewa taron manyan jami’an na Amurka, da Australia, da India, da Japan, na cike da salon cacar baka, da siyasar wariya.

Bangaren Sin na ganin cewa, yankin tekun Asiya da Fasifik, zai samu ci gaba mai dorewa ne kadai, idan an gudanar da hadin gwiwa, tsakanin kasashen shiyyar, maimakon hada wani gungu na kawance, domin yin fito na fito.

Ko shakka babu, lokaci zai kara fayyace cewa, duk wasu dabaru da ake gudanarwa domin cimma moriyar kashin kai, da nuna wariya, ba za su haifar da da mai ido ba. Kaza lika mafi yawan kasashe dake yankin Asiya da Fasifik, za su ci gaba da samun ikon fada a ji a nan gaba, a wannan yanki karkashin manufar zaman tare a gida guda.  (Saminu)