logo

HAUSA

An kammala aikin gini mafi tsayi a gabashin Afirka

2022-02-14 10:52:20 CRI

An kammala aikin gini mafi tsayi a gabashin Afirka_fororder_0e3dc735097647748ef7db166d2846ff

A jiya Lahadi, an kammala aikin ginin sabuwar helkwatar bankin kasuwancin kasar Habasha, aikin da kamfanin kasar Sin ya dauki nauyin ginawa, wanda kuma ya kasance gini mafi tsawo a gabashin nahiyar Afirka. Firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed Ali da jakadan kasar Sin a kasar Mr. Zhao Zhiyuan sun halarci bikin kaddamar da ginin.

Ginin dai ya kasance a cibiyar kasuwanci ta birnin Addis Ababa, kuma kamfanin CSCEC ne ya fara daukar nauyin ginawa tun daga watan Yulin shekarar 2015.

A jawabin da ya gabatar, firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed Ali ya taya murnar kaddamar da ginin, inda ya ce, yadda aka kaddamar da wannan kyakkyawan ginin a daidai lokacin cika shekaru 80 da kafuwar bankin kasuwancin kasar ya shaida aniyar kasar na zamanintar da harkokin bankinta.

Sai kuma babban darektan bankin kasuwancin Habasha ya ce, sabon ginin zai inganta aikin bankin, tare da samar da fasahohin zamani ga bangaren gine-gine na kasar. (Lubabatu)