logo

HAUSA

Kantinan sayar da abincin kasar Sin sun bunkasa fiye da gabanin barkewar annobar COVID-19

2022-02-14 17:03:50 CRI

Kantinan sayar da abincin kasar Sin sun bunkasa fiye da gabanin barkewar annobar COVID-19_fororder_1

Masu hikamar magana na cewa, “sai da ruwan ciki ake jan na rijiya.” Hakika, abinci shine ginshikin rayuwar duk wata halitatta a doron kasa, kuma rayuwa ba ta yiwuwa ba tare da abinci da kuma abin sha ba. A kasar Sin fannin abinci wani babban jigo ne da shugabanni da mabiya ke dora muhimmanci kansa. Alal misali, koda a karshen wannan mako, wani rahoto ya bayyana cewa, kamfanonin dake mallakar kantinan sayar da abinci sun samu gagarumar bunkasuwar da ta kai matsayin koli wacce har ma ta zarce makamancin lokacin gabanin barkewar annobar COVID-19. Rahoton kan batun masana’antu ya bayyana cewa, kamfanonin gidajen sayar da abinci na kasar Sin sun samu gagarumar bunkasuwa a shekarar 2021 duk da matsin lambar da annobar COVID-19 ke haifarwa, inda aka samu karuwar bude sabbin gidajen sayar abinci da kashi 25.5 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin shekarar 2020. A bisa rahoton, jimillar sabbin kamfanonin sayar da abinci miliyan 2.36 aka samu a shekarar 2021, kamar yadda babban kamfanin sayar da abinci ta intanet na kasar Sin Meituan ya bayyana. Rahoton kamfanin ya ce, kasar Sin tana samun karuwar harkokin hada-hadar gidajen sayar da abinci a shekarun baya bayan nan, inda adadin ke cigaba da karuwa daga kashi 12.8 bisa 100 a shekarar 2018 zuwa kashi 15 bisa 100 a shekarar 2020. Har ma an bayyana cewa, fannin masana’antun samar da abincin kasar Sin sun mayar da komadarsu a shekarar 2021 wanda ya kai matsayin na gabanin barkewar annobar, inda jimillar kudaden shigar fannin ya karu da kashi 18.6 bisa 100 idan an kwatanta da na shekarar da ta gabata wanda adadin ya kai yuan triliyan 4.69, kwatankwacin dala biliyan 736. Koda yake, wannan cigaban da ake samu ba zai rasa nasaba da irin jajurcewa da kuma kwararan matakai da mahukunta kasar ke dauka don ganin fannin samar da abinci ya samu gagarumin tagomashi ba. Alal misali, ko da a karshen wannan mako, firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya jaddada aniyar tallafawa fannin aikin gona domin tabbatar da cigaban bunkasa samar da hatsi wanda ya zarta kilogram biliyan 650 cikin shekara guda. A cewarsa, ya zama wajibi a kara azama don tallafawa aikin gona, da bada tabbacin samar da kayan amfanin gona, da tabbatar da daidaita farashin kayan amfanin gonar, da kuma tabbatar da fara ayyukan noman bazara a kan lokaci. Dama dai masu hikimar magana na cewa, “bayan wuya sai dadi.”(Ahmad Fagam)