logo

HAUSA

Sin ta tallafawa shirin COVAX da dala miliyan 100

2022-02-14 19:34:33 CRI

Sin ta tallafawa shirin COVAX da dala miliyan 100_fororder_汪文斌-2

A yau Litinin 14 ga watan Fabarairu ne, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya shaidawa taron manema labarai cewa, kasar Sin ta cika alkawarin da ta dauka, inda a ranar Juma’a 11 ga wata, ta gabatarwa shirin samar da rigakafi na COVAX da gudummawar dalar Amurka miliyan 100, kudaden da za a yi amfani da su wajen rarraba rigakafin annobar COVID-19 ga kasashe masu tasowa.

Wang Wenbin, ya ce tun a yayin taron kasa da kasa game da hadin gwiwar samar da rigakafi da ya gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya alkawarta wannan tallafi. Kuma kamar yadda aka gani a yanzu, Sin ta cika wannan alkawari yadda ya kamata.

Da aka yi masa tambaya game da matsayin kadarorin babban bankin kasar Afghanistan da aka daskarar kuwa, Wang ya ce kadarorin da darajar su ta kai dalar Amurka biliyan 7, wadanda aka rike a matsayin diyyar harin ta’addanci na ran 11 ga watan 9 na shekarar 2001 da ya auku a birnin New York na Amurka, kadarori ne na al’ummar kasar Afghanistan, don haka ya kamata a mayar wa ‘yan kasar hakkin su, domin su samu damar inganta rayuwa.

Da ya tabo batun gasar Olympics ta hunturu da birnin Beijing ke karbar bakunci yanzu haka kuwa, Wang Wenbin ya ce gasar ta samu tagomashi, inda ake nuna ta ta kafofin talabijin masu matukar inganci. Kuma duk da yake ana ci gaba da fuskantar yaduwar annobar COVID-19 a sassan duniya, hakan bai karya lagon gasar ba, inda take ci gaba da gudana cikin yanayi na nishadantawa, da bunkasa abota, karkashin wasannin kankara da na dusar kankara dake gudana tsakanin al’ummun sassan kasashen duniya masu yawa.  (Saminu)