logo

HAUSA

Yawan Amurkawan dake kallon gasar Olympic ta lokacin sanyi dake gudana a Beijing ya zarce miliyan 100

2022-02-13 16:41:15 CRI

Yawan Amurkawan dake kallon gasar Olympic ta lokacin sanyi dake gudana a Beijing ya zarce miliyan 100_fororder_下载

Jiya Asaba, an yi taron manema labarai karo na 8 a cibiyar watsa labarai ta gasar Olympic ta lokacin hunturu dake birnin Beijing. Kakakin kwamiti mai kula da harkokin Olympic Mark Adams, ya bayyana cewa, yawan mutanen dake kallon gasar ya kai sabon matsayi.

Kakakin ya ce, yawan Sinawa kusan miliyan 515 sun kalli gasar ta CMG kafin ranar 10 ga wata, adadin Amurkawan da suka kalli gasar ya haura miliyan 100 ta tashar NBC. Jami’an IOC da kwamitin shirya gasar na Beijing sun amsa tambayoyin da ‘yan jarida suka yi musu game da ba da kulawa da hidimomi ga ‘yan wasan. Ban da wannan kuma, jami’in kwamitin Beijing ya yi bayani kan na’urorin kauyukan Olympic da abinci, da ayyukan jin dadin zaman rayuwa da ayyukan jiyya da dai sauransu.

Shugaban kula da kauyen Olympic Shen Qianfan ya ce, kauyen ya kasance daki mafi girma da ba a yi takara a ciki ba, da kuma gidan ‘yan wasan gasar, sannan an kawata dakunan cin abinci tare da samar da gasashiyyar agwagwa mai salon Beijing da Jiaozi da sauran nau’ikan abincin kasar Sin, ta yadda ‘yan wasa za su more wasanninsu tare da fahimtar al’adun kasar Sin musamman ma sabuwar shekarar damisa bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. (Amina Xu)