logo

HAUSA

Gwamnatin Amurka ta yi rashin dattaku na kwace kudaden ceton rayuka a Afganistan

2022-02-13 16:42:20 CRI

Gwamnatin Amurka ta yi rashin dattaku na kwace kudaden ceton rayuka a Afganistan_fororder_amurka

A ranar 11 ga wata, shugaban kasar Amurka Joe biden, ya sa hannu kan wani umurni game da kudin babban bankin kasar Afganistan dake Amurka da aka hana amfani da su, inda aka bayyana cewa, Amurka za ta raba kudin da yawansa ya kai dala kusan biliyan 7 kasu biyu, wato za a yi amfani da rabinsa domin biyan kudin diyya ga wadanda suka rasa rayuka ko suka ji rauni yayin hadarin jirgin saman da ya faru a ranar 11 ga watan Satumban shekarar 2001, saura rabi kuma, gwamnatin Amurka za ta yi amfani da kudin domin samar da tallafi ga al’ummun Afganistan, amma ba za ta tattauna batun da gwamnatin Taliban ba.

Da zarar al’ummun kasa da kasa suka ji labarin, sai sun kadu matuka, saboda sun ga gwamnatin Amurka ta kwace kudin ceton rayukan al’ummun Afganistan a fili!

A tsakiyar watan Agustan bara, bayan da dakarun Taliban suka mamaye birnin Kabul, fadar mulkin kasar Afganistan, daga lokacin gwamnatin Amurka ta hana a yi amfani da kudin babban bankin kasar dake ketare, ciki har da dala biliyan 7 da aka adana a kasar ta Amurka, hakika kudin babban bankin Afganistan, kudi ne na al’ummun kasar, bai dace Amurka ta yi amfani da su ba, lamarin dai, ya bayyanawa duniya karara rashin dattakun gwamnatin Amurka. (Jamila)