logo

HAUSA

Yan siyasar Amurka na cikin damuwa saboda rashin barkewar yaki tsakanin Rasha da Ukraine

2022-02-13 20:35:42 CRI

Yan siyasar Amurka na cikin damuwa saboda rashin barkewar yaki tsakanin Rasha da Ukraine_fororder_rasha

A ranar 12 ga watan Fabrairu, shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya sake yin ikirari a yayin zantawarsa ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin cewa, idan har Rasha ta kaiwa Ukraine hari, Amurka da kawayenta za su yiwa Rashar taron dangi har sai sun tabbatar da ta dandana kudarta. Game da wannan batu, Putin ya jaddada cewa, Rasha ta kasa gane dalilin da ya sa Amurka take fitowa baro-baro tana bayyanawa kafafen yada labarai kalaman karya cewa, Rasha tana shirin yiwa Ukraine mamaya.

Duk da kasancewar Amurkar tana ci gaba da rura wutar yaki, amma ra’ayoyin da dama daga cikin manyan masu sharhi kan al’amurran kasa da kasa sun yi amanna cewa, barazanar yiwuwar barkewar yaki a sakamakon takun sakar dake tsakanin Rasha da Ukrain, ba wani mai girma ba ne, saboda dukkan bangarorin da abin ya shafa suna da masaniyar cewa, yaki zai iya ruruta wutar wani mummunan tashin hankalin da ba za a iya kashe wutarsa ba.

To kuwa tun da haka ne, mene ne ya sa Amurka take ci gaba da zuzuta batun cewa, Rasha za ta yiwa Ukraine mamaya? Da farko, Amurka tana kokarin kusanto da kasashen Turai jikinta ta hanyar kambama batun barazanar Rasha.

Na biyu, “yin hasashe" ta hanyar kalaman neman haddasa yaki da maganganun neman takalar fada, wani sanannan makirci ne da Amurka ke amfani da shi. A cewar rahoton, bayan barkewar rikicin Ukraine, kasar Amurka ta aike da tarin makaman yaki masu yawa ga Ukraine. Lallai akwai wata boyayyar manufa da rukunin dakarun sojojin kasar Amurka ke neman fakewar da ita karkashin wannan batu.(Ahmad)