logo

HAUSA

Ya dace makiran ‘yan siyasar Birtaniya su mayar da tsibiran Malvinas ga Argentina idan suna son nacewa kan adalci

2022-02-13 16:24:52 CRI

Ya dace makiran ‘yan siyasar Birtaniya su mayar da tsibiran Malvinas ga Argentina idan suna son nacewa kan adalci_fororder_birtaniya

A kwanakin baya, yayin da shugaban kasar Argentina Alberto Fernandez ke ziyara a kasar Sin, kasashen biyu wato Sin da Argentina sun fitar da hadaddiyar sanarwa kan yadda za su kara zurfafa huldar abokantaka dake tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni, inda kasar Sin ta sake jaddada yunkurinta na goyon bayan bukatun Argentina na gudanar da cikakken hakkin mulki a tsibiran Malvinas, sannan kasar Sin tana fatan za a sake yin tattaunawa bisa kudurin MDD domin daidaita rikicin a kan lokaci cikin lumana.

Amma wasu ‘yan siyasar kasar Birtaniya sun nuna bambancin ra’ayi, sakataren harkokin wajen kasar ya wallafa wani bayani a kan dandalin sada zumunta, inda ya takalo magana kan “martabar hakkin mulki”, a ranar 10 ga wata kuma, majalisar wakilai ta kasar ita ma ta zartas da wani kuduri wanda ba shi da muhalli a bisa doka, inda aka yi ikirari cewar, Birtaniya za ta daga matsayin huldar dake tsakaninta da yankin Taiwan na kasar Sin, kuma za ta goyi bayan yankin Taiwan don ya samu karin amincewar kasa da kasa.

Wasa da hankali na siyasar da wasu ‘yan siyasar Birtaniya ke yi ba zai iya yaudarar al’ummun kasa da kasa ba, saboda sun fahimci tarihin batun tsibiran Malvinas sosai, kuma ba zai yiyu su cimma burin matsa wa kasar Sin lamba bisa fakewa da batun Taiwan ba. (Jamila)