logo

HAUSA

Masana'antun abincin kasar Sin sun bunkasa da kashi 25.5 a 2021

2022-02-13 16:02:50 CMG

Masana'antun abincin kasar Sin sun bunkasa da kashi 25.5 a 2021_fororder_0213-dakin cin abinci-Ahmad

Wani rahoto kan masana’natu ya bayyana cewa, kamfanonin gidajen sayar da abinci na kasar Sin sun samu gagarumar bunkasuwa a shekarar 2021 duk da matsin lambar da annobar COVID-19 ke haifarwa, inda aka samu karin rejistar bude gidajen abincin da kashi 25.5 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin shekarar 2020.

Jimillar sabbin kamfanonin sayar da abinci miliyan 2.36 aka samu a shekarar 2021, kamar yadda babban kamfanin sayar da abinci ta intanet na Meituan ya bayyana.

Rahoton kamfanin ya ce, kasar Sin tana samun karuwar harkokin hada-hadar gidajen sayar da abinci a shekarun baya bayan nan, inda adadin ke cigaba da karuwa daga kashi 12.8 bisa 100 a 2018 zuwa kashi 15 bisa 100 a shekarar 2020.

Fannin masana’antun samar da abincin kasar Sin sun mayar da komadarsu a 2021 wanda ya kai matsayin na gabanin barkewar annoba, inda jimillar kudaden shigar fannin ya karu da kashi 18.6 bisa 100 idan an kwatanta da shekarar da ta gabata wanda adadin ya kai yuan triliyan 4.69, kwatankwacin dala biliyan 736, kamar yadda alkaluman hukumomin kasar suka bayyana.(Ahmad)

Ahmad