logo

HAUSA

Kasar Sin ta gabatar da darasi na musamman na yaki da talauci ga Afrika

2022-02-11 10:33:49 CRI

Kasar Sin ta gabatar da darasi na musamman na yaki da talauci ga Afrika_fororder_220211-zambia-Faeza1

Shugaban kasar Zambia, Hakainde Hichilema ya ce, kasar Sin da sauran kasashen Asiya sun gabatarwa Zambia da ma sauran kasashen Afrika, darussa na musamman game da yaki da talauci. Yana mai ba kasashen Afrika shawarar koyi da dabarun wajen kyautata rayuwar al’ummominsu.

Hakainde Hichilema ya bayyana haka ne yayin taron da shugaban kasar kan yi a kowacce shekara da jami’an diflomasiyya dake kasar.

A cewarsa, akwai abubuwa da dama da Zambia da sauran kasashen Afrika za su iya koyo daga nahiyar Asiya, kuma sun shirya fadada lalubo wadannan dabaru.

Ya ce Zambia za ta ci gaba da girmama huldarta da kasashen Asiya da kara hadin kai musamman a bangaren samar da makamashi mai tsafta da kuma tallafin ilimi. Har ila yau, za ta ci gaba da hada hannu da kasashen na Asiya ta hanyoyi da dama kamar na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen Afrika na FOCAC.  (Fa’iza Mustapha)