logo

HAUSA

An shirya tunkarar yanayi mai tsanani yayin wasannin Olympics na Beijing

2022-02-11 14:25:27 CRI

An shirya tunkarar yanayi mai tsanani yayin wasannin Olympics na Beijing_fororder_220211-Olympics-Faeza3

Yayin da ake hasashen samun dusar kankara da karuwar yanayin sanyi a karshen wannan makon a biranen Beijing da Zhangjiakou, kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing ya ce ya shirya daukar matakan tabbatar da gudanar wasanni ba tare da tangarda ba, da kuma tabbatar da lafiya da tsaron dukkan jami’ai, duk tsananin yanayi.

Kakakin kwamitin Zhao Weidong, ya ce suna girmama yanayin halitta da kokarin tabbatar da gudanar wasannin kamar yadda aka tsara, a lokaci guda kuma, za su tabbatar da lafiya da tsaron yan wasa da jami’ai da masu aikin sa kai.

Ya kara da cewa, domin shiryawa tsanantar yanayi, kwamitin zai yi aiki da karin hasashen yanayi masu inganci.

A cewarsa, masu hasashen yanayi za su bayyana kididdigarsu ta yanayi ga masana na hukumomin kasa da kasa, inda su kuma, za su tantance bukatar sauya wuraren wasanni da kuma yadda za a yi. (Fa’iza Mustapha)