logo

HAUSA

Afrika na kan hanyar shawo kan tsaikon da COVID-19 ta haifar

2022-02-11 11:18:24 CRI

Afrika na kan hanyar shawo kan tsaikon da COVID-19 ta haifar_fororder_220211-Africa COVID19-Faeza2

Kimanin shekaru 2 bayan bullar cutar ta farko a nahiyar Afrika a ranar 14 ga watan Fabrerun 2020, nahiyar na kan hanyarta ta kawo karshen tsaikon da annobar ta haifar.

Daraktar hukumar lafiya ta duniya a nahiyar Afrika, Matshidiso Moeti ce ta bayyana haka, yayin wani taro ta kafar bidiyo a jiya, inda ta ce duk da annobar COVID-19 za ta dauki lokaci mai tsawo kafin a dakile ta baki daya, akwai kyakkyawan fata na ganin bayanta. Ta ce a bana, za a iya kawo karshen tsaiko da kalubalen da ta haifar, tare da ganin dawowar al’amura kamar yadda suke a baya. Tana mai cewa, ci gaba da sa ido kan cutar, abu ne mai muhimmanci.

Ta ce cikin shekaru 2 da suka gabata, an samu bullar cutar har zagaye 4 a Afrika, inda kowane zagaye ke kai wa matsayin koli ko adadin mace-mace ke zarce na zagayen da ya gabata.

Har ila yau, ta ce duk da matsalolin da ake fuskanta, ciki har da na rashin daidaito wajen rabon rigakafi, an tunkari annobar ta hanyar juriya da jajircewa, da suka samo asali daga tarihin nahiyar na dakile barkewar annoba. Ta kara da cewa, an samu gagarumin ci gaba a kokarin nahiyar Afrika na takaita yaduwar annobar.  (Fa’iza Mustapha)