logo

HAUSA

Sama da ’yan ta’adda dubu 30 sun mika wuya ga sojoji a arewa maso gabashin Najeriya

2022-02-11 11:34:38 CRI

Sama da ’yan ta’adda dubu 30 sun mika wuya ga sojoji a arewa maso gabashin Najeriya_fororder_220211-boko haram-Ahmad4

Wani babban jami’i ya ce, sama da ’yan ta’adda dubu 30 da suka hada da mayakan Boko Haram da na ISWAP, a ranar Alhamis sun mika wuya ga sojojin Najeriya a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya fadawa manema labarai bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari game da halin da ake ciki a shiyyar, gwamnan ya ce, an fara samun farfadowar zaman lafiya yayin da hukumomin tsaro ke ci gaba da daukar matakan dakile ayyukan ’yan ta’adda a shiyyar.

Sai dai gwamna Zulum, bai bayyana takamamman lokacin da ’yan ta’addan suka fara mika wuyan ba.

Gwamnan ya ce, nan ba da jimawa ba ayyukan ta’addanci za su zama tarihi a shiyyar, inda ya bayyana matakin mika wuyan da cewa gagarumin cigaba ne. (Ahmad)