logo

HAUSA

Gasar Amurka, gasa ce cikin lumana, ko yunkurin hana bunkasuwar sauran kasashe?

2022-02-11 11:15:01 CRI

Gasar Amurka, gasa ce cikin lumana, ko yunkurin hana bunkasuwar sauran kasashe?_fororder_220211-sharhi-maryam-hoto

Kwanan baya, majalisar dokokin kasar Amurka ta zartas da “Dokar Gasa ta Amurka ta Shekarar 2022”, domin tabbatar da matsayin kasar na kan gaba a fannonin masana’antu, kirkire-kirkire, da karfin tattalin arziki. Amma, cikin wannan doka, kasar Amurka ta yi suka kan manufofin kasar Sin wajen neman ci gaba, da wasu harkokinta na cikin gida. Hakika dai, nufinta shi ne hana ci gaban kasar Sin bisa hujjar yin gasa. Shi ya sa, ake ganin cewa, wannan dokar da kasar Amurka ta fidda, doka ce ta hana ci gaban sauran kasashe.

Kasar Amurka tana da ’yancin neman bunkasuwa, amma, ba ta hanyar hana bunkasuwa da bata sunan kasar Sin ba, balle ma, tsoma baki cikin harkokin gidan kasar, da kuma bata moriyarta.

Shirin karfafa dangantakar dake tsakanin kasar Amurka da lardin Taiwan na kasar Sin, da aka ambata cikin wannan doka, ya keta manufar kasar Sin kasa daya tak, da kuma ka’idar sanarwoyin hadin gwiwa guda uku da aka kulla tsakanin kasar Sin da da kasar Amurka. Lamarin da ya nuna cewa, wasu ’yan siyasan kasar Amurka suna neman hana bunkasuwar kasar Sin baki daya, ta hanyar bata yanayin siyasa a yankin Taiwan na kasar.

Amma, kasar Amurka ba za ta cimma nasarar mugun burinta ba, domin, tabbas, kasar Sin za ta mai da martani ga wadanda suka tsoma baki cikin harkoki gidanta, da kuma neman bata moriyarta. Da fatan kasar Amurka za ta iya dakatar da wannan doka nan take, da kuma daidaita dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin da idon basira. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)