logo

HAUSA

Kwamitin wasannin Olympics na Uganda ya yabawa Sin bisa shirya wasanni yayin da ake fama da COVID-19

2022-02-11 11:05:27 CRI

Kwamitin wasannin Olympics na Uganda ya yabawa Sin bisa shirya wasanni yayin da ake fama da COVID-19_fororder_220211-uganda olympics-Faeza4

Shugaban kwamitin shirya wasannin Olympics na kasar Uganda, Donald Rukare, ya jinjinawa kasar Sin game da yadda ta shirya kayatacciyar gasar Olympics ta lokacin hunturu, yayin da ake fama da annobar COVID-19.

Donald Rukare, ya shaidawa Xinhua cewa, shirya wasanni a lokacin da ake fama da annoba, abu ne mai wahala.

Ya ce ana gudanar da wasanni a lokacin annobar COVID-19, wanda ba lokaci ne mai sauki ba, amma duk da haka, bikin bude wasannin ya kayatar sosai.

Ya kara da cewa, suna bibiyar wasannin kuma suna ganin yadda ’yan wasa ke taka rawar gani. Inda ya ce ya ga yadda wani matashin dan wasa mai shekaru 18 yake taka rawar gani dake karya matsayin bajinta. (Fa’iza Mustapha)