logo

HAUSA

Dakarun Najeriya sun dakile fasa-kwaurin hauren giwa da dabbar pangolin

2022-02-11 14:19:25 CRI

Dakarun Najeriya sun dakile fasa-kwaurin hauren giwa da dabbar pangolin_fororder_220211-nigeria ivory smuggle-Ahmad5

Dakarun tsaron gwamnatin Najeriya sun kama mutane hudu da ake zargi da yunkurin fataucin hauren giwa da dabbar pangolin wadanda darajarsu ta kai kusan dalar Amurka miliyan 7.4, kamar yadda hukumomin kasar suka bayyana.

A sanarwar da hukumar kwastam ta kasar NCS ta fitar ta ce, dakarun musamman na hukumar NCS sun kama mutanen da ake zargi da fasa-kwaurin a ranar 2 ga watan Fabraru, a tashar ruwan Lekki dake Lagos, birnin kasuwancin Najeriya.

Hukumar NCS ta ce, an gudanar da ayyukan ne karkashin hadin gwiwa da hukumar yaki da masu farautar dabbobin daji ta kasar. (Ahmad)