logo

HAUSA

Sin na adawa da ra’ayin ministan harkokin wajen Lithuania game da kasar Sin

2022-02-10 21:40:12 CRI

Rahotanni na cewa, yayin da ministan harkokin wajen kasar Lithuania ke ziyara a kasar Australia, ya yi kira ga dukkan duniya da su yi adawa da ayyukan keta hakkin dan Adam da Sin da Rasha suke aikatawa.

Game da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya yi nuni a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, ya kamata kasar Lithuania ta rungumi gaskiya, ta gyara kuskurenta, ta komawa manufar “kasar Sin daya tak a duniya”, kuma ta dakatar da matakai marasa dacewa, da hada kan sauran kasashe, wajen adawa da kasar Sin. (Zainab)