logo

HAUSA

Da Ruwan Ciki Akan Ja Na Rijiya

2022-02-10 17:19:28 CRI

Da Ruwan Ciki Akan Ja Na Rijiya_fororder_hatsi

Sanin kowa ne cewa, duk wani ci gaba da duk wata kasa za ta samu, yana yin tasiri ne idan kasar ta iya cimma nasarar wanzar da rayuwar al’ummun ta, musamman ta fannin samar da abinci da tsaro, kafin duk wani mataki na inganta rayuwar al’umma.

A baya bayan nan, daya daga muhimman batutuwa dake jan hankulan masharhanta, shi ne yadda yankin kahon Afirka ke fuskantar kamfar abinci, sakamakon fari mai tsanani dake addabar yankin wanda ya haifar da karancin yabanya a gonaki, da kuma farin dango da suka addabi yankin a wasu lokuta.

A cewar shirin samar da abinci na duniya WFP, bisa kiyasi, mutane miliyan 13 na fama da yunwa a kasashen Habasha, da Kenya da Somalia, yayin da yankin na kahon Afrika ke fama da matsanancin rashin ruwan sama mafi muni da yankin ya fuskanta, tun bayan shekarar 1981. Alkaluma sun nuna yadda wannan yanki ya fuskanci damina 3 a jere, ba tare da isasshen ruwan sama ba, inda girbin amfanin gona ya yi kasa da kaso 70 bisa dari idan an kwatanta da na shekarun baya.

Wannan matsala dai na ci gaba da haifar da ta’azarar mutuwar dabbobi, da karancin amfanin gona ga al’ummu mazauna yankunan da ibtila’in ya fi shafa. Tuni kuma shirin na WFP ya fara azamar samar da tallafin abinci mai gina jiki ga dumbin al’ummun yankin.

Yayin da WFP ke shirin ba da tallafi, a daya hannun, akwai bukatar kara mayar da hankali kan matakan dakile sauyin yanayi, a matakai na kasa da kasa da na shiyya shiyya.

Ya kamata kasashen duniya, musamman masu karfin tattalin arziki su kara azama, wajen sauke nauyin dake wuyan su, na tallafawa kasashe masu tasowa, musamman na nahiyar Afirka, da tallafin kudaden kare muhalli, da muhallin halittu, da dakile kwararar hamada. Kaza lika su kara daukar matakan rage fitar da nau’o’in hayaki mai gurbata muhalli. Wadannan da ma sauran matakai dake kunshe cikin yarjejeniyar kare muhalli ta Paris, za su taimaka matuka, wajen ingiza nasarar takaita mummunan tasirin sauyin yanayi dake addabar sassa daban daban na duniya, ciki har da yankin na kahon Afirka.

A cikin nahiyar Afirka kuwa, kamata ya yi mahukunta sun gaggauta hada karfi da karfi, wajen aiwatar da matakan kariya ga muhalli, da dazuzzuka, da ruwaye, da kyautata ingancin iskar. Kafa ganuwar bishiyoyi ta hanyar dashen itatuwa ma, na cikin muhimman matakai da masana ke cewa zai taimakawa nahiyar Afirka, wajen shawo kan mummunan tasirin sauyin yanayi.

Bugu da kari, kamar yadda kasar Sin ta sha tallafawa kasashen nahiyar da shawarwarin kwararu, da dabarun noma na zamani, da ilimin shuka tsirrai masu bukatar ruwan sama kalilan, kamata ya yi sauran manyan kasashen duniya ma dake da kwarewa a wannan fage su bi sahu, wajen ba da gudummawar su ga ci gaban noman zamani a Afirka, duba da cewa, duk wani ci gaba da nahiyar za ta samu, zai biyo bayan samar da isasshen abinci ne, kamar dai yadda Bahaushe kan ce “Da ruwan ciki akan ja na rijiya”. (Saminu Alhassan)