logo

HAUSA

IOM: An mayar da bakin haure ’yan Mali 111 zuwa gida a makon jiya

2022-02-10 11:13:09 CRI

IOM: An mayar da bakin haure ’yan Mali 111 zuwa gida a makon jiya_fororder_0210-Ahmad5-Malian immigrants

Hukumar kula da bakin haure ta kasa da kasa IOM ta sanar cewa, an mayar da bakin haure 111 zuwa kasarsu ta Mali daga kasar Libya wadanda suka mika kansu a makon jiya.

Kawo yanzu, sama da bakin haure 800 ne suka amince a mayar da su zuwa kasashensu na asali daga kasar Libya karkashin shirin mayar da bakin hauren da suka mika kansu zuwa kasashensu a wannan shekarar.

Libya ta kasance a matsayin wata matattarar dubban bakin haure dake neman tsallaka tekun Mediterranea zuwa kasashen Turai.

A cewar hukumar IOM, a shekarar 2021, jimillar bakin haure 32,425 aka ceto kuma aka mayar da su Libya, yayin da wasu 662 sun mutu, kana wasu 891 sun bace a tekun Libya a babbar hanyar tekun Mediterranea. (Ahmad)