logo

HAUSA

Tsohuwar tauraruwa Shui Qingxia ta zamo jigon nasarar kungiyar kwallon kafar mata ta kasar Sin

2022-02-10 19:54:55 CRI

Tsohuwar tauraruwa Shui Qingxia ta zamo jigon nasarar kungiyar kwallon kafar mata ta kasar Sin_fororder_shui

Babbar mai horas da kungiyar ‘yan wasan kwallon kafar mata ta kasar Sin Shui Qingxia, ta sake samun karin nasara a tarihin aikin ta na horas da ‘yan wasa, inda a baya bayan nan ta jagoranci kungiyar Sin zuwa lashe kofin nahiyar Asiya na AFC, bayan shekaru 16.

Masharhanta na cewa, tarihi ya sha nuna kwarewar Shui Qingxia wajen tsara dabarun samun nasara, kamar dai yadda wasu masu fashin baki suka wallafa bayan zantawa da kocin, gabanin buga wasan karshe na gasar ta AFC. Wasu ma na cewa, wata kila Shui Qingxia na da nasibi ne na musamman na lashe kofin Asiya ajin mata na AFC. Ko da yake wannan na iya zama hasashe kawai, amma ga duk wanda ya nazarci tarihin aikin horas da ‘yan wasa na Shui, zai gaskata wannan hasashe.

A matsayin ta na mambar rukunin da ake wa lakabi da "golden generation", a tawagar kwallon kafar mata ta Sin a shekarun 1990, Shui ta daga kofin har karo 5 cikin shekaru 11, ba tare da fuskantar koma baya ba, wanda hakan ya sanya tawagar ta Sin zama mafi samun nasara a tsakanin kulaflikan kasashen Asiya a wannan gasa.

Amma fa duk da irin nasarori da wannan kungiya ta Sin ta cimma, ta hanyar lashe kofuna da dama, Sin ba ta dandana farin cikin lashe kofin na Asiya ba tun daga shekarar 2006, lokacin da ta dauki na karshe kafin na bana.

Tawagar “Steel Roses” ta Sin, ta samu koma baya cikin shekaru 10 da suka gabata, kuma Sin ta fita daga rukunin kungiyoyin da sauran kasashe masu fafatawa a gasar ke tsoron haduwa da ita. Karon karshe da tawagar ta yi rashin nasara mai yawa shi ne a shekarar 2020, yayin gasar Olympic ta birnin Tokyo, karkashin tsohuwar kocin tawagar Jia Xiuquan, inda a lokacin ta kwashi rashin nasara a hannun kungiyar kasar Brazil da ci 5-0, kana ta buga kunnen doki da ci 4-4 da Zambia, kaza lika ta yi rashin nasara da ci 8-2 da Netherlands.

Daga nan sai kocin kungiyar kwallon kafar mata ta Shanghai Shui ta karbi ragamar kasar ta Sin, a ranar 18 ga watan Nuwambar 2021, a lokacin da ba wanda ke tsammanin za ta iya kawo wani sauyi na daban, a gasar cikin kofin Asiya da aka buga a India watanni 2 da rabi, bayan kama aikin ta. Shui ta yi namijin kokari wajen lashe kofin na AFC karo na 9, da Sin ta lashe bisa jajircewa da himma da kwazo.

An ta ganin sakwanni a shafukan sada zumunta na Sin dake yaba kwazon koci Shui, inda daya daga cikin su ke cewa "Ta lashe kofin AFC ta hanyar sauya ‘yan wasa! Ta zama tauraruwar kasar Sin!".

Wani kuma na cewa "Ta lashe kofin AFC a matsayin ‘yar wasa da kuma koci!".

Wasu sun rika mamakin yadda Shui ta samar da babban sauyi ga kungiyar ta Sin, suna ganin ga duk koci da za ta maye gurbin Jia Xiuquan, abu ne mai wahala ta iya farfado da kungiyar daga koma bayan da ta fuskanta a baya, baya ga batun karancin lokacin aiwatar da sauyin. Wasu na ganin Sin ta rasa irin damar da ta samu a baya, ta cimma manyan nasarori a kwallon kafar mata, har ma suna ganin kamata ya yi kungiyar ta Sin ta mayar da hankali ga lashe gasar cin kofin duniya, ta hanyar gwada kwazon ta a gasar ta cin kofin Asiya, maimakon dagewa wajen kokarin lashe kasar ta AFC.

Hakika abubuwan da suka faru a kasa da wata guda da ya gabata, sun nuna Shui a matsayin koci mafi dacewa da horas da tawagar ta Sin.

Bayan buga matsakaitan wasanni a zagaye na farko na gasar, tawagar Sin ta farfado sosai a wasannin zagaye na 2 na gasar, inda ta yi nasara kan kasar Japan a wasan kusa da kusan na karshe, ta bugun daga-kai-sai-mai tsaron gida, a wasan karshe kuma, ta doke koriya ta kudu da ci 3-2, duk da cewa Koriya ce ta fara zura kwallaye 2 a ragar Sin.

Shui ta bayyana bayan kammala wasan cewa, "Lashe wannan gasa ba hanya ce ta sauwake mana komai da komai ba, dole ne mu ci gaba da kara kwazon mu na taka leda da karfafa tunani".

Ma’anar sunan "Shui", da dangin ta suka rada mata shi ne "Ruwa" da harshen Sinanci, amma kuma a wajen ‘yan wasan da take horaswa, koci Shui na da tsanani da karfin ikon ba da horo, wanda hakan ya ba ta karbuwa sosai tsakanin ‘yan wasan ta.

Wani abu na daban, da dama ba su sani ba game da Shui shi ne, ta fara sana’ar wasannin ta ne daga filin tsere, inda ta ke shiga wasannin tsalle mai nisa, da gudun yada kanin wani, tun lokacin tana karatu, shekaru 6 nan kafin a ba ta shawarar fara buga kwallon kafa.

Lokacin da ta cika shekaru 17, ta riga ta makara. Kuma shekaru da dama bayan zabin sauya wasan da take shiga, ta rika samun kokwanto. Ta kan ce "Na rika damuwa, game da dalilin da zai sa a bar mace ta rika buga kwallon kafa, amma dai ba wani abu. "

Duk da kasancewar ta fara koyon kwallon kafa daga tushe, ta yi ta kokarin koyon nau’oin wasa da kwallo, kuma nan da nan Shui ta yi fice tsakanin daruruwan dalibai dake koyon kwallon kafa a babbar tawagar birnin Shanghai.

Shekara daya bayan nan, sai aka gayyace ta shiga tawagar kwallon kafar Sin, wadda ta lashe lambar azurfa a gasar Olympic ta birnin Atlanta, wadda aka gudanar a shekarar 1996.

Baya ga hakan, Shui ta kasance daya daga Sinawa mata da suka fara buga kwallo a kasashen waje, inda ta taka leda a kungiyoyin kasar Japan guda 2.

Lokacin da take buga wasa, Shui na da tsattsauran ra’ayin kula da horo. Kuma a matsayin ta na Koci, an rika kallon ta a matsayin mai tsauri kan ‘yan wasa. Amma a yanzu, ta yi sanyi, inda take kara maida hankali ga gina karfin tunanin ‘yan wasan da take horaswa.

Shui ta ce "Matasan ‘yan wasa na yanzu, suna da banbanci sosai da na da, jumla daya, tana iya sauya yanayin kwazon su, don haka suna bukatar karfafa masu gwiwa. Kafin bugun daga-kai-sai-mai tsaron gida da kungiyar kasar Japan, na shaida musu cewa, su kwantar da hankalin su, su karfafa zuciyar su, za mu yi nasara tun da mun farke kwallaye har 2 kafin tashi wasan".

Duk da an koma zango na biyu na wasan karshe, bayan an jefa wa kasar Sin kwallo biyu a raga, Shui ta ci gaba da karfafa gwiwar ‘yan wasan ta da kada su karaya. A lokaci guda kuma, Shui ta yi wasu sauye sauye, inda ta cire tautaruwar kungiyar Wang Shuang, bayan ta ji rauni da Zhang Yanlin, wadda ta taka rawar gani wajen baiwa bangaren na Sin damar rama kwallayen da aka zura masa.

Game da hakan, Shui ta ce "Na yi farin ciki, musamman ganin yadda ‘yan wasan mu suka yi kwazo, duk da rashin nasarar mu a farko, ina godiya gare su, sun fitar da dukkanin mu kunya".

Wannan nasara ta zamo tamkar wani haske ne da tawagar kwallon kafar mata ta Sin ta samu, bayan gamuwa da tarin kalubale. Yayin da Sin ke fatan sake dawowa saman teburin kwallon kafa a matakin kasa da kasa, zuwan koci Shui, ya zama tamkar sara ne a kan gaba.