logo

HAUSA

Gasar wasanni Olympic ta Beijing ta lokacin hunturu na gudana cikin nasara

2022-02-09 08:52:24 CRI

Yanzu haka dai gasar Olympic ta lokacin hunturu ta 2022 dake gudana yanzu, bisa jagorancin birnin Beijing, na ci gaba da gudana lami lafiya, kuma kasashen duniya sun rungumi wannan gasa cike da fatan alheri. Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da sauran shugabannin duniya da dama, sun bayyana farin cikin su da kaddamar da gasar cikin lumana, sun kuma yi amannar cewa, gasar za ta bunkasa ruhin ta na hada kan al’ummun duniya, na sada zumunta, da aiki tare, domin shawo kan kalubalen da ke addabar daukacin bil adama.

Gasar wasanni Olympic ta Beijing ta lokacin hunturu na gudana cikin nasara_fororder_0209世界22006-hoto1

A makon farko na bude gasar ta Olympic, kasashen Sin, da Sweden, kwamitin Olympics na Rasha na kan gaba wajen lashe lambobin yabo da aka tanada. Ya zuwa ranar 20 ga watan nan na Fabarairu kuma, lokacin da za a kammala wannan gasa, duniya za ta ga zakarun da za su kara lashe lambobin yabo na gwaninta a wannan kasaitacciyar gasa.

Yanzu haka dai, ana fafata wasanni nau’o’i da dama irin na lokacin hunturu, da suka hada da na kankara da dusar kankara, kuma tuni ’yan wasa 2,891 daga sassan kasashe 91 suka hallara, domin neman lashe lambobin yabo mafi yawa da aka tsara lashewa a makamantan wannan gasa da suka gabata a baya.

Gasar wasanni Olympic ta Beijing ta lokacin hunturu na gudana cikin nasara_fororder_0209世界22006-hoto3

Gasar Olympic ta lokacin hunturu ta 2022 da birnin Beijing ke karbar bakunci a bana, ta zo daidai lokacin da kungiyar kwallon kafar mata ta kasar Sin ta lashe kofin kwallon kafar nahiyar Asiya ko AFC karo na 9, bayan ta doke Koriya ta kudu a wasan karshe da aka buga a kasar Indiya a karshen mako.

Gasar wasanni Olympic ta Beijing ta lokacin hunturu na gudana cikin nasara_fororder_0209世界22006-hoto2

Kaza lika gasar ta zo daidai lokacin da nahiyar Afirka ta kammala gasar cin kofin kwallon kafar Afirka na hukumar AFCON, wanda ya gudana a kasar Kamaru. A wannan karo dai a karon farko, Senegal ta lashe wannan kofi, bayan ta doke Masar a bugun daga kai sai mai tsaron gida a karshen makon jiya. Yanzu haka dai Masar ce ke rike da kofin na AFCON guda 7, sai Ghana da Kamaru masu biyar biyar, akwai Najeriya da Aljeriya dake da kofuna uku uku, sai Janhuriyar diflomasiyyar Congo mai kofi 2, yayin da Senegal ta kafa tarihin daukar kofin na bana da kofi 1. (Saminu Hassa, Ahmad Fagam, Sanusi Chen)