logo

HAUSA

Jami’an wanzar da zaman lafiya na MDD da dakarun DRC na kara sintiri a lardin Ituri

2022-02-09 10:07:24 CRI

Jami’an wanzar da zaman lafiya na MDD da dakarun DRC na kara sintiri a lardin Ituri_fororder_220209-DRC-Faiza2

Jami’an wanzar da zaman lafiya na MDD da dakarun Jamhuriyar Demokradiyyar Congo na kara sintiri a kusa da sansanin ’yan gudun hijira na lardin Ituri, da aka kai wa hari a makon da ya gabata.

Stephane Dujarric, kakakin Sakatare Janar na MDD ya ce, jami’an na MDD sun ce akwai karuwar fargaba a lardin na Ituri dake arewa maso gabashin kasar, biyo bayan harin da aka kai makon da ya gabata, kan sansanin ’yan gudun hijira na Savo, wanda ke da nisan kilomita 8 daga kudu maso gabashin Djugu.

A cewar kakakin, Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya yi tir da harin na ranar 1 ga wata, wanda ya yi sanadin rayukan fararen hula a kalla 58 tare da raunata wasu 36.

Shirin wanzar da zaman lafiya na MDD dake Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, da ake kira da MONUSCO sun yi musayar wuta da ’yan tawayen CODECO, arangamar da ta auku yayin wani aikin bincike a yankin Uzi na lardin Ituri. (Fa’iza Mustapha)