Nasiru Umar Tambuwal: Ina kira ga matasan Najeriya su tashi tsaye don neman ilimi da aikin yi
2022-02-09 14:19:54 CRI
Nasiru Umar Tambuwal, dan asalin Sokoto ne wanda ya yi shekaru biyar da rabi yana neman karo ilimi a kasar Sin. A yayin zantawarsa da Murtala Zhang kwanan nan, ya bayyana fahimtarsa game da al’adun gargajiya da halayen mutanen kasar Sin.
Nasiru Tambuwal, wanda a yanzu haka yake karatun digiri na biyu a birnin Shenyang na lardin Liaoning dake arewacin kasar ta Sin, ya yi kira ga al’umma da su tantance gaskiyar labaran da suka ji game da kasar Sin daga wasu kafafen yada labaran kasashen yammacin duniya, saboda gani ya kori ji.(Murtala Zhang)