logo

HAUSA

Abin Jinjinawa Ne Yadda Aka Kaddamar Da Gasar Wasannin Olympics Ta Hunturu Ta Beijing 2022

2022-02-09 09:44:47 CMG

Abin Jinjinawa Ne Yadda Aka Kaddamar Da Gasar Wasannin Olympics Ta Hunturu Ta Beijing 2022_fororder_1

Kamar dai yadda aka shirya a ranar Juma’a 4 ga watan Fabrairu na wannan shekara ne aka kaddamar da gasar wasannin Olympics ta hunturu a babban filin wasa dake Beijing, babban birnin kasar Sin. Ita wannan gasar wasanni ta Olympics dai ana yinta ne duk shekaru hudu hudu. Wannan shekarar dai nauyin bakuncin gasar ya sauka ne a kan birnin Beijing. An kuma bude gasar a dai dai lokacin da Sinawa ke shagulgulan bikin bazara, biki mafi kasaita da ke alamanta shiga wata sabuwar shekara bisa kalandarsu ta gargajiya. Bukukuwan sun hadu biyu ke nan!

Ita dai wannan gasar wasanni wacce ke kawo mutane daga kasashe dabam-dabam tare, muhimmancinta shi ne karfafafa hadin gwiwar kasashen duniya da al’ummarsu. Taken Olympic na wannan shekarar dai shine “Mu rungumi makomarmu tare”. Don haka, duk da kaurace wa halartar gasar da wasu kasashe kalilan suka yi, babu abin da ya kawo cikas, kuma ba su hana bukin budewar kayatarwa ba, saboda kowa ya gane cewa siyasa ce kawai wadanda suka yi kira da a kaurace suke amfani da ita don cimma burinsu. Tun kafin ranar bude wasannin, shugabannin kasashen duniya da na kungiyoyi na kasa da kasa suke ta turo sakonnin fatan alheri da cimma nasara a wasannin na Olympics ta hunturu. Kamar dai yadda shugaban kwamitin shirya gasar Olympic na kasa da kasa wato IOC Thomas Bach ya fada “Da hadin gwiwar kowa da kowa, za mu rubuta tarihi a harkar wasanni”. Wannan dai ya nuna cewa bukatar al’ummar duniya shi ne hadin gwiwa da martaba juna, ba cece kuce ba.

Hakazalika kasashe kimanin 90 ne tare da ’yan wasa kusan dubu 3 suka sauka birnin Beijing domin shiga gasar wasannin na kan kankara da na kan dusar kankara. Duk kasashen da suka kauracewa bukin bude gasar, sun turo ’yan wasanninsu wanda shi ne ya kara nuna cewa duk siyasa ce ake amfani da ita.

Manyan baki da suka halarci bukin bude wasannin sun hada da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da babban sakataren majalisar dinkin duniya UN Antonio Guiterres da shugaban kasar Masar Abdel Fatah el-Sisi da firaministan Pakistan Imran Khan da shugaban kasar Kazakhstan Kassim Jomart Tokayev da babban direktan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Gebreyesus da basaraken hadaddiyar daular larabawa UAE da dai sauransu. Baya ga haka, kasashe da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 66 ne suka aiko da wakilansu a wannan taron bukin bude wasannin wanda shi ne manuni a kan gamsuwa da goyon bayan da kasar Sin ta samu a sakmakon bakuncinta na gasar wasannin Olympics ta hunturu 2022.

Duk da babu yanayin hunturu mai sanyi da dusar kankara a nahiyar Afirka, wani abin alfahari shi ne kasashen Afirka na Najeriya, Ghana, Madagaska, Morroco da Eritrea sun shiga gasar wasannin Olympics din. Wannan ma ya nuna cewa kasashen nahiyar Afirka ba’a bar su a baya ba domin kasancewarsu a wannan gasar wasannin, ba wai don samun gwala gwalai ba ne kawai, domin shiga harkokin wasanni ne da habaka fannin wasannin motsa jiki na kasa da kasa da kawo zamantakewar al’umma na sassan duniya da kuma samun abokai.

Abubuwan da na lura kuma masu ban sha’awa a wannan Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing 2022 shi ne sababbin fasahohi da na’urori da aka kawo a wannan karon. Akwai layin dogo mai sauri da aka gina na musamman mai na’urar 5G wanda zai yi sufurin ’yan wasa da ’yan jarida daga Beijing zuwa Zhangjiakou. Bayan wannan akwai sauran abubuwan zamani a duk filayen wasanni da ake yi a kan kankara ko na kan dusar kankara.

Masu shirye-shiryen wannan gasar wasannin ta bana dai sun tabbatar da nasara da gamsuwa ga ’yan wasa da mabiya wasannin. A matuka akwai abubuwan sha’awa tun daga ranar bude gasar wasannin ya zuwa yanzu da wasannin suka kankama. Tabbas kuma wannan abin jinjinawa ne ma shugaba Xi Jinping, da kwamitin Olympics ta duniya IOC da kwamitin shirye-shirye na Beijing 2022 a kan nasarar da ka samu tun farkon fara shirya wannan hidima. Ina fatan za’a yi gasar wasannin cikin lafiya da lumana.(Sharhi daga Lawal Sale)(Kamfanin Xinhua ya samar da hoto)

Lawal Sale