logo

HAUSA

Wakilin Sin: Sin na goyon bayan matsayin Iran na daidaita batun nukiliyarta ta hanyar tattaunawa

2022-02-09 10:02:40 CRI

Wakilin Sin: Sin na goyon bayan matsayin Iran na daidaita batun nukiliyarta ta hanyar tattaunawa_fororder_wang qun

Bangarorin da suka kulla yarjejeniyar nukiliya ta Iran, sun gudanar da tattaunawa karo na 8, jiya Talata a birnin Vienna, fadar mulkin kasar Austria, domin ci gaba da tattaunawa kan batun Amurka da Iran su sake aiwatar da yarjejeniyar. Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD wanda ya shiga tattaunawar Wang Qun, ya bayyana cewa, kasar Sin ta goyi bayan matsayin kasar Iran na nacewa kan daidaita batun nukiliyar ta hanyar tattaunawa.

Wang Qun ya kara da cewa, ya dace bangarori daban daban su girmama sakamakon da aka samu, su kuma kara cimma matsaya, ta yadda za su daddale yarjejeniyar kan lokaci.

Kana Wang Qun ya jaddada cewa, tarihin tattaunawa kan batun nukiliyar Iran ya shaida sau da dama cewa, tattaunawa ita ce mafita daya kacal kan batun, yana mai fatan sassan da abin ya shafa za su nace kan manufar daidaitawa ta hanyar siyasa. Ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da hada hannu tare da su domin ciyar da tattaunawar gaba yadda ya kamata. (Jamila)