logo

HAUSA

Masani a Nijeriya: Gasar Olympics ta hunturu ta Beijing ta nuna ruhin dan adam na tunkarar wahalhalu da kalubale

2022-02-09 10:54:28 CRI

Masani a Nijeriya: Gasar Olympics ta hunturu ta Beijing ta nuna ruhin dan adam na tunkarar wahalhalu da kalubale_fororder_220209-Onunaiju-Faeza

Daraktan cibiyar binciken harkokin kasar Sin ta Nijeriya, Charles Onunaiju, ya jinjinawa muhimmacin wasannin Olypmlics na lokacin hunturu na Beijing. Yana mai cewa, yayin da ake zaman dar-dar a wasu sassan duniya da fuskantar yaduwar cutar COVID-19, nasarar bude wasannin Olympics na Beijing, ya bayyana ruhin dan Adam na tunkarar kalubale da wahalhalu. Haka kuma ya daukaka ruhin wasannin ga duniya.

Charles Onunaiju ya bayyana haka ne cikin sharhinsa mai taken “Muhimmancin Wasannin Olympics na Hunturu na Beijing” wanda jaridar People’s Daily ta kasar ta wallafa. Ya kuma bayyana cewa, karbar bakuncin wasannin da Sin ta yi, ba taimakawa wajen karfafa hadin kai a duniya kadai zai yi ba, har ma da nuna cewa babu wani kalubale da zai kawo wa dan adam cikas a kokarinsa na neman hadin kai.

Har ila yau, ya ce taken wasannin na “Mu Gudu Tare mu Tsira Tare”, ya dace da tunanin gina al’umma mai kyakkaywar makoma ga daukacin bil adama. (Fa’iza Mustapha)