Mene ne dalilin da ya sa shawarar ziri daya da hanya daya ta kara habaka?
2022-02-09 13:45:42 CRI
Matukin babbar motar dakon kaya na kasar Argentina Maxilimi Luhan ya taba bayyana cewa, tun bayan da aka kaddamar da jiragen kasa na kasar Sin, kudin da ake kashewa wajen jigilar kayayyaki a layin dogo na Saint Martin ya ragu da kaso 40 bisa dari, kana wasu karin kamfanoni sun zabi jiragen kasa yayin da suke jigilar kayayyaki. Hakika kasashen Sin da Argentina suna gudanar da hadin gwiwa wajen gina manyan gine-ginen more rayuwar jama’a bisa shawarar ziri daya da hanya daya, sakamakon haka, kayayyakin aikin gonan Argentina sun nuna fiffikon farashi a kasuwar kasa da kasa.
Abu mafi faranta ran Luhan shi ne, a kwanakin baya, shugaban kasarsa Alberto Fernandez ya sa hannu kan takardar fahimtar juna dangane da shiga shawarar ziri daya da hanya daya, yayin da yake ziyarar aiki a kasar Sin. (Jamila)