logo

HAUSA

Amurka Ta Zama Babbar Kwabo

2022-02-09 19:06:51 CRI

Amurka Ta Zama Babbar Kwabo_fororder_Amurka-1

Amincewa da manufar kasar Sin daya tak a duniya, ita ce tubali ko sharadin duk wata hulda da wata kasar waje za ta kulla da kasar Sin. Wannan dai yana nufin, amincewa Taiwan Ko Hong Kong, dukkansu wani bangare da ba za a iya raba su da kasar Sin ba. A matsayin Amurka na wadda take kiran kanta da babbar kasa a duniya, ya kamata a ce tana sane da wannan ko ma in ce tana kiyaye wannan ka’ida. Sai dai abin kunya shi ne, yadda take ci gaba da zubar da kimarta a idon Sinawa har ma da daukacin duniya. Har kullum, burin kasar Sin shi ne, hawa teburin sulhu, domin a daddale batutuwa, a cimma matsaya mai gamsarwa ga dukkan bangarori. Sai dai, duk wannan yunkuri bai gamsar da Amurka ba, inda take gaban kanta wajen ta da rikici da kakaba takunkumai da shiga sharo ba shanu, da ma duk wani nau’i na takala.

A baya-bayan nan Amurkar ta yi alkawarin aiwatar da manufar Sin daya taka a duniya, kuma ba za ta goyi bayan masu rajin balle tsibirin Taiwan daga Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin ba, amma kuma abin takaici shi ne, bayyanar shirinta a ranar Litinin da ta gabata, na cewa, za ta sayar da hidimomin tsaro da makamai ga yankin Taiwan, wadanda darajarsu ta kai dala miliyan 100. Kuma, wannan shi ne karo na biyu da ta yi hakan. Duk wani mai bibiyar huldar Sin da Amurka, ya san cewa, Amurka ba ta cika alkawurran da take dauka na kyautata hulda tsakanin kasashen biyu, ko kuma tana amai tana lashewa, lamarin da ya mayar da ita babbar kwabo. Haka kuma, a bayyane yake, ba ta muradin ganin zaman lafiya da dinkewar kasar Sin. Tana sane cewa, ayyukan nata za su kawo hatsaniya, amma, ta gaza la’akari da hakan, idan ta mayar da hankali wajen cimma moriyarta, wanda kuma mumunan tasirinsa, zai shafe ta da al’ummarta.

Kamata ya yi, babba ya rika zama abun koyi ga na kasa da shi.  Kamata ya yi a ce  sabbin kalubalen da suke kunno kai a duniya, su zama darasi ga Amurka, na ganin an gudu tare an tsira tare, maimaikon kawo rarrabuwar kawuna. A matsayinsu na manyan kasashe, kamata ya yi Sin da Amurka su zama abin koyi ga sauran kasashe. Ya kamata idan aka cimma yarjejeniya, to a aiwatar da ita, ba wai a rika saba alkawari ba, domin wannan, ba zai taba kai duniya ga samun kyakkyawar makomar da ake bukata ba, ko kuma zaman lafiya da fahimtar juna da ake muradi.

Kasar Sin dai ta sha nanata cewa, ba za ta taba kasa a gwiwa ko gazawa wajen kare cikakken iko da yankuna da tsaro da muradun jama’arta ba. Kuma a shirye take ta mayar da martani kan duk wani yunkuri na lalata moriyarta. (Fa’iza Mustapha)