logo

HAUSA

Sayar da makamai ga Taiwan ya sake shaida yunkurin Amurka na gurgunta zaman lafiya a zirin

2022-02-09 09:43:49 CRI

Sayar da makamai ga Taiwan ya sake shaida yunkurin Amurka na gurgunta zaman lafiya a zirin_fororder_amurka

A ranar 7 ga wata, gwamnatin kasar Amurka ta tsai da kudurin sayar da “hidimar aikin makamai masu linzami na Patriot” da “na’urorin sa ido kan filin daga”, wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka miliyan 100 ga yankin Taiwan na kasar Sin. Wannan ne karo na biyu da gwamnatin Biden ta sayar da makamai ga Taiwan. Matakin da ta dauka ya sake shaida yunkurinta na gurgunta zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Taiwan.

Batun Taiwan yana da muhimmanci matuka yayin da ake gudanar da hulda tsakanin kasar Sin da Amurka, gwamnatin Amurka ita ma ta fahimci lamarin, don haka ta yi alkawarin aiwatar da manufar kasar Sin daya kacal a duniya sau da dama, kana ta yi alkawari cewa, ba za ta goyi bayan yunkurin ‘yancin kan Taiwan ba. Amma abubuwan da suka faru sun shaida cewa, Amurka ba ta cika alkawarin da ta yi ba. Misali Amurka ta tura jiragen ruwan yaki zuwa zirin Taiwan, ta kuma sayar da makamai ga Taiwan din, hakika duk wadannan matakan da Amurka ta dauka za su jefa yankin Taiwan cikin mawuyancin yanayi.

Dole ne a cimma burin dunkulewar kasar Sin, kuma babu wanda zai hana hakan. Ya zama wajibi Amurka ta aiwatar da manufar kasar Sin daya kacal a duniya, ta soke shirinta na sayar da makamai ga yankin Taiwan, tare kuma da katse huldar aikin soja dake tsakaninta da Taiwan. Haka kuma, ta daina gurgunta moriyar kasar Sin ta hanyar amfani da ‘yan aware masu neman ‘yancin kan Taiwan, in ba haka ba, ya zama wajibi kasar Sin ta dauki mataki mai karfi, domin kare hakkin mulki da moriyarta na tsaro. (Jamila)