Kwalliya Za Ta Biya Kudin Sabulu Wajen Tabbatuwar Ruhin Wasannin Olympics Na Habaka Zaman Lafiya A Duniya
2022-02-08 17:43:21 CRI
Tun lokacin da kasar Sin ta samu damar karbar bakuncin wasannin Olympics na lokacin hunturu na 2022, ta daura damarar ganin wasan ya gudana cikin nasara, inda har ta sanya burin ganin al’ummun Sinawa miliyan 300 sun halarci wasan kankara. Zuwa yanzu dai, an fara ganin cikar wannan buri, ganin yadda Sinawa manya da kanana, suka fara, ko kara sha’awar wasannin kankara. Kasancewar dabbobi ne ke alamta kalandar gargajiya ta kasar Sin, a duk lokacin da aka shiga sabuwar shekara, kayayyakin dake alamta dabbar shekarar ne suka fi samun karbuwa. Sai dai a bana, shiga sabuwar shekarar Damisa, ta zo a daidai da lokacin wasannin Olympics na hunturu na Beijing, lamarin da ya sa sayen kayayyakin dake alamta wasannin suka zarce na sabuwar shekarar Damisa. Wato dai, bude wasannin Olympics ko kuma karbar bakuncin wasannin a nan kasar Sin, ya bude wata kofa ta samun habakar sayayya a bangaren da ya shafi wasannin kankara. A ganina, irin ci gaba da aka samu, ya biyo bayan irin goyon bayan da al’ummar Sinawa ke ba gwamnati har ma da yadda suke matukar kishin kasarsu. Yadda gwamnatin ke sanya al’umma a gaban komai, haka al’umma ke bata goyon bayan a duk wani abu da ta sanya gaba. Yadda suke sayayya ya habaka tattalin arzikin bangaren dake da alaka da kankara, kamar wuraren wasanni da kayayyakin da ake amfani da su wajen wasan kankara da yawon shakatawa da sauransu, wanda kuma zai kai ga habakar tattalin arzikin kasar baki daya. Daga karshen bara zuwa yanzu, an yi kiyasin Sinawa miliyan 346 sun halarci wasannin da suka shafi kankara, adadin da ya dauki kaso 24.56 na daukacin al’ummun kasar, wanda kuma ya zarce burin kasar na mutane miliyan 300. Wannan kuma babbar alama ce dake nuna cewa, Sinawa suna goyon bayan wasannin dake gudana a kasarsu, har ma da maraba da bude kofarsu ga ‘yan wasa daga sassa daban-daban na duniya, duk da barazanar da ake fuskanta na yaduwar annobar COVID-19. Lallai ko shakka babu, kwalliya za ta biya kudin sabulu, wato za a ga tabbatuwar ruhin wasannin na habaka zaman lafiya da fahimtar juna da kuma hadin kai a duniya. (Fa’iza Mustapha)