logo

HAUSA

Ma’aikatar wajen Sin: An zabi masu mika wutar yula ta wasannin Olympics ta hanyar da ta dace

2022-02-08 11:08:08 CRI

Ma’aikatar wajen Sin: An zabi masu mika wutar yula ta wasannin Olympics ta hanyar da ta dace_fororder_zhao

An zabi ‘yar wasan kabilar Uygur Dinigeer Yilamujiang, ta kasance mai mika wutar yula ta wasannin Olympics na lokacin sanyi na birnin Beijing, lamarin da ya jawo hankalin wasu mutane. Kan wannan batun, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana yayin taron ganawa da manema labarai jiya cewa, an tsara ma’auni mai inganci yayin da ake gudanar da aikin zabar masu mika wutar yula ta wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing.

Zhao ya kara da cewa, bisa ka’idar wasan Olympics, Dinigeer Yilamujiang tana da ikon shiga gasa da kuma bikin bude ta, inda ya jadada cewa,“An mika wutar yula tsakanin zuriyoyi uku, wato tsoffi da masu matsakacin shekaru da kuma matasa, domin nuna gadon ruhin wasannin Olympics, muna farin cikin ganin ‘yan wasan kabilu daban daban da suka hada da Dinigeer Yilamujiang, sun shiga gasannin da ake gudanarwa, wanda ke nuna cewa, kasar Sin tana kokari matuka wajen raya wasan kankara, da kara karfin lafiyar al’ummun kasar, wanda kuma ke nuna cewa, kasar Sin babban iyali ne dake samun zaman jituwa tsakanin kabilu daban daban.” (Jamila)