logo

HAUSA

Al’ummar Ghana na sa rai ga nasarar dan wasan kasar daya tilo a wasannin Olympics na hunturu na Beijing

2022-02-08 11:56:49 CRI

Al’ummar Ghana na sa rai ga nasarar dan wasan kasar daya tilo a wasannin Olympics na hunturu na Beijing_fororder_220208-Ghana-Faeza5

Da dan wasa daya tilo dake wakiltar kasar a gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing, wasu al’ummar kasar Ghana, na sa ran ganin nasarar dan wasan zamiya kan tuddan kankara na Alpine, wato Carlos Mader, ya kafa tarihi a kasar ta yammacin Afrika.

Wasu mutane sun shaidawa Xinhua cewa, suna da kyakkyawan fata cewa, dan wasan daya, dake wakiltar kasar a gasar wasannin Olympics na hunturu, zai yi irin kokarin da takwaransa Samuel Takyi ya yi, a wasan Olympics na lokacin zafi da aka yi bara a kasar Japan, inda ya lashe lambar tagulla a wasan damben boxing.

Eric Tordzro, wani malamin wasannin motsa jiki a makarantar Chemu dake Tema na yankin gabashin kasar Ghana, ya ce yana sa ran Carlos Mader, zai lashe a kalla lambar Tagulla a wasanni Olympics na hunturu, tun da ya samu gogewa a kasashen waje, kan wasa da ba a yi a kasarsa dake da yanayi na zafi.

Carlos Mader, mazauni kasar Switzerland zai fatafata ne a wasan zamiyar alpine na Giant Salom, ajin maza, inda zai zama dan wasa na 3 da ya wakilci kasar Ghana a wasannin Olympics na lokacin hunturu, bayan Kwame Nkrumah-Acheampon da ya wakilci kasar a wasannin shekarar 2010 da aka yi a Vancover da kuma Akwasi Frimpong, da ya wakilci kasar a wasannin PyeongChang na shekarar 2018. (Fa’iza Mustapha)