'Yan wasan kasar Sin sun lashe lambobin zinari da na azurfa a tseren kankara na mita 1000 ajin maza
2022-02-08 09:02:56 CRI
A ci gaban wasannin Olympics na hunturu da ke gudana yanzu a birnin Beijing, a jiya da dare, an gudanar da gasar karshe ta wasan tseren kankara na gajeren zango na mita 1000 ajin maza, inda ‘yan wasa na kasar Sin Ren Ziwei da ma Li Wenlong suka lashe lambobin zinari da na azurfa.(Lubabatu)