logo

HAUSA

’Yan sandan Nijeriya sun dakile wani harin ’yan bindiga a jihar Kogi

2022-02-08 10:03:47 CRI

Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta ce jami’anta, sun dakile yunkurin harin ’yan bindiga kan wani ofishinsu dake jihar Kogi na arewa maso tsakiyar kasar, inda suka kashe daya daga cikin maharan.

Kakakin ’yan sandan jihar Kogi, William Oyve-Aya, ya shaidawa manema labarai a Lokoja, babban birnin jihar a jiya Litinin cewa, ’yan bindigar sun kai harin ne da yammacin ranar Lahadi, kan ofishin ’yan sanda dake yankin Okene na jihar, sai dai ’yan sandan dake bakin aiki a lokacin, sun katse hanzarinsu.

Williams Aya ya kara da cewa, maharan sun kai harin ne suna harbin kan mai uwa dawabi tare kuma da ababen fashewa. Yana mai cewa, jami’an ’yan sanda sun mayar da martani, inda suka harbe daya daga cikin ’yan bindigar, lamarin da ya tilasta musu tserewa, tun ma kafin a tura karin ’yan sanda wurin. (Fa’iza Mustapha)