logo

HAUSA

Tattalin arzikin kankara ya samu ci gaba yayin bikin bazara na kasar Sin

2022-02-08 10:14:37 CRI

Tattalin arzikin kankara ya samu ci gaba yayin bikin bazara na kasar Sin_fororder_bingdundun

Yayin da ake murnar bikin bazara na shekarar Damisa na gargajiyar kasar Sin, kayayyakin masu alamar musamman na wasannin Olympics na lokacin sanyi na birnin Beijing, da ake kira Bingdundun sun fi na Damisa samun karbuwa, har ma samun su na da matukar wahala. Ana iya cewa, kasuwar sayayya ta hutun bikin bazara na kasar Sin ta kara habaka yayin da ake kallon wasannin Olympics na lokacin sanyi, tattalin arzikin bangaren wasannin kankara yana ingiza ci gaban tattalin arzikin kasar ta Sin.

A shekarar 2015, lokacin da kasar Sin ta gabatar da rokon shirya wasannin Olympics na lokacin sanyi, an yi alkawari cewa, za a yi kokari domin al’ummun Sinawa miliyan 300 su halarci wasan kankara, kuma zuwa yanzu, an riga an cimma wannan burin. Ya zuwa watan Oktoban bara wato shekarar 2021, adadin Sinawa wadanda suka halarci wasan kankara ya kai miliyan 346, adadin da ya kai kaso 24.56 bisa dari na daukacin al’ummun kasar Sin. Daga wasan kankara, da yawon shakatawa dake shafar kankara, da sana’o’in samar da kayayyakin wasan kankara, da kuma hada-hadar kudi dake shafar sana’o’in kankara, an lura cewa, sana’o’in bangaren kankara na kasar Sin sun samu ci gaba daga dukkan fannoni.

A halin yanzu, duk da cewa, annobar cutar COVID-19 tana ci gaba da bazuwa a sauran sassan duniya, kasuwar sayayya ta kasar Sin tana kara habaka. Dalili shi ne, a ko da yaushe gwamnatin kasar Sin tana sanya lafiyar al’ummunta a gaba da komai, kana tana daukar matakan da suka dace yayin kandagarkin annobar, da kokarin ingiza ci gaban tattalin arzikin kasar, wadanda suka nuna cewa, kamfanonin kasa da kasa su ma suna iya cin gajiya daga “damarmakin kasar Sin” sakamakon karuwar bukatun babbar kasuwar kasar.(Jamila)