logo

HAUSA

Sharhi: Shirme ne yadda aka bayyana ‘yar wasan Xinjiang mai mika wutar yula a matsayin martani da Sin ta mayar ga kasashen Yamma

2022-02-08 21:20:59 CRI

Sharhi: Shirme ne yadda aka bayyana ‘yar wasan Xinjiang mai mika wutar yula a matsayin martani da Sin ta mayar ga kasashen Yamma_fororder_20220205120237692

Yanzu haka gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu na gudana yadda ya kamata a birnin Beijing, wanda ake sa ran za ta zama mai matukar nasara a tarihin wasannin Olympics. Kamar yadda a kan ce, kyakkyawan mafari shi ne rabin nasara. Bikin bude gasar da aka gudanar a daren ranar 4 ga wata har yanzu ya kasance mai burgewa, musamman ma a lokacin da sannu a hankali aka daga wata babbar da’ira mai suffar kasko zuwa sama, a filin gudanar da bikin bude gasar, kana ‘yan wasan kasar Sin Dinigeer Yilamujiang da Zhao Jiawen suka daga wutar yola tare, inda suka yi tattaki suka mika ta tsakiyar da’irar, sa’an nan da’irar ta mika saman filin wasa mai suffar shekar tsuntsu dake birnin Beijing, a matsayin wata alama ta kaddamar da wannan gasa. Hakan ya burge jama’ar kasashe da dama, inda hakan ya nuna tamkar an kunna wutar da ke cikin al’ummar duniya ne, masu hada kai da rungumar makomarsu tare.

Sai dai abin bakin ciki shi ne wasu kafofin yada labarai na kasashen yamma ba su mai da hankali a kan kyakkyawan sakon da bikin ya isar ga al’ummun duniya, da ma gasar ita kanta ba, a maimakon haka, sun mai da hankali ne a kan ‘yar wasa Dinigeer Yilamujiang, wadda ta fito daga jihar Xinjiang ta kasar Sin, har ma sun rika bayyana ta a matsayin martani da kasar Sin ta mayar ga kasashen yamma wadanda suka kauracewa gasar. Kamfanin dillancin labarai na Bloomberg ya ruwaito cewa, “Dinigeer ‘yar wasa ce mai gwaninta, amma bai kamata a kyale matsayinta na ‘yar Uygur ba.”  Sai kuma mai gabatar da shiri a kafar NBC na Amurka, Savannah Guthrie, wadda a yayin da take bayani ta ce, wannan ya kasance “wata sanarwar da kasar Sin ta fitar”, kuma “martani ne da ta mayar ga kasashen yamma”, sai dai furucin ya janyo mata matsala, har ma wasu kafofin yada labarai na kasashen yamma suka zarge ta da “bauta wa gwamnatin kasar Sin”. Baya ga haka, jaridar NewYork Times ta ce wai an tilastawa wannan ‘yar wasan Xinjiang yin wannan aiki.

Sharhi: Shirme ne yadda aka bayyana ‘yar wasan Xinjiang mai mika wutar yula a matsayin martani da Sin ta mayar ga kasashen Yamma_fororder_20220205142012457

Lallai, su wadannan kafofin yada labarai kwata kwata sun siyasantar da bikin, kamar dai yadda ‘yan siyasar kasashen su suka yi tun farkon fari, wato fakewa da sunan kare hakkin bil Adam don kauracewa gasar, a wani kokari na haifar da matsala ga bunkasuwar kasar Sin.

Sai dai a gani na, shirme ne kawai, kuma abun ban dariya ne. Shin ‘yan wasa ‘yan kabilar Uygur na Xinjiang ba su cancanci zama masu mika wutar yula ta gasar Olympics ba ne? Ko kuma mika wutar yula shi ma wani nau’i ne na aikin keta hakkin dan Adam?

Hakan ya sa wasu masu bibbiyar shafukan yanar gizo sun kasa hakuri, inda suka ce, abun alfahari ne ga ‘yan wasa su kasance masu kunna wuta a bikin bude gasar Olympic, don haka shirme ne yadda kafofin yada labarai na kasashen yamma suka ce an tilastawa ‘yan wasan yin hakan. Wasu kuma sun ce, idan babu ‘yan wasan Uygur a wajen bikin, lalle NewYork Times za ta ce, kasar Sin ta hana ‘yan wasan Uygur su fito. Lallai kome ya faru ba za ta ji dadi ba.

Sharhi: Shirme ne yadda aka bayyana ‘yar wasan Xinjiang mai mika wutar yula a matsayin martani da Sin ta mayar ga kasashen Yamma_fororder_20220205132203107

A game da wannan, kakakin kwamitin kula da wasannin Olympics na kasa da kasa (IOC) Mark Adams, ya bayyana a gun taron manema labarai cewa, Dinigeer ‘yar wasan gasar Olympics ta lokacin hunturu ce, don haka tana da hakkin halartar dukanin bukukuwan da aka shirya, kuma yadda aka zabe ta a matsayin mai mika wutar yula, ba shi da alaka da inda aka haife ta. A daya bangaren kuma, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya ce, “An mika wutar yula tsakanin zuriyoyi uku, wato tsoffi da masu matsakacin shekaru da kuma matasa, domin nuna gadon ruhin wasannin Olympics, muna farin cikin ganin ‘yan wasan kabilu daban daban da suka hada da Dinigeer Yilamujiang, sun shiga gasannin da ake gudanarwa, wanda ke nuna cewa, kasar Sin tana kokari matuka wajen raya wasan kankara, da kara karfin lafiyar al’ummun kasar, wanda kuma ke nuna cewa, kasar Sin babban iyali ne dake samun zaman jituwa tsakanin kabilu daban daban.”

Daga nata bangaren, malama Dinigeer mai shekaru 20 da haihuwa ta ce, “Yadda na kasance a bikin bude gasar zai dada ba ni kwarin gwiwa a kwanaki na gaba, wanda zan rike a zuci a tsawon rayuwata.”

Gasar Olympics gasa ce ta wasanni, bai kamata a cusa siyasa a cikin ta ba.

A yayin da annobar Covid-19 ke addabar duniya, yadda kasar Sin ta gudanar da gasar kamar yadda aka alkawarta, ya samar da damar karfafa hadin kan al’ummun kasashe daban daban, don tinkarar kalubalen da suke fuskanta, wanda kuma gudummawa ce da kasar Sin ta samar wa duniya. Don haka muke lallashin ‘yan siyasa, da kafofin yada labarai na wasu kasashe, da su daina siyasantar da gasar, su mai da hankali a kan sakon da gasar ke isarwa, da ma gasar da ke gudana, kuma in da gaske ne suna “kulawa da” hakkin dan Adam na wasu kasashe, lallai ya kamata su kara nuna sahihancinsu. (Lubabatu)